1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Hu Jintao a Faransa

November 5, 2010

Shugaban Faransa, Nicholas Sarkozy da kuma takwaransa na China wato Hu Jintao sun ƙarfara dangantakar kasuwanci tsakanin ƙasashensu.

https://p.dw.com/p/PzK6
Nicholas Sarkozy da Hu JintaoHoto: AP

Shugabannin ƙasashen Faransa da China sun rattaɓa hannu akan wasu jerin yarjejeniyoyin cinikayya da suka kai darajar biliyon 14 na Euro. Daga cikinsu kuwa har da odar manyan jiragen sama ƙirar Airbus na Faransa na jimmilar Euro 10 da Hu jintao ya yi. Wasu mahimman al'amura da suka ɗauki hankali Shugaba Hu jintao da kuma Nicholas Sarkozy a ganawar da suka yi a birnin Paris, har da batun darajar takardar kuɗin Yuan na ƙasar China da kuma batun tsaro.

Ziyarar kwanaki uku ta Shugaba Hu jintao, ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron G20 a makon mai zuwa a birnin Seoul da ke Koriya ta Kudu. Sai dai kuma sauran ƙungiyoyin masu fafutuka da ma 'yan siyasa sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawarsu da ziyarar shugaban ƙasar ta China saboda ƙaurin suna da ƙasar ta yi wajen tauye haƙƙin bil-Adama.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas