1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Jack Straw zuwa Najeriya

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 14, 2006

Batutuwa dake kan ajandar wannan ziyarar ta Jack Straw sun hada da halartar tattaunawar zaman lafiya na Darfur dake gudana a Abuja, wadda Burtaniya take ganin yana tafiyar hawainiya

https://p.dw.com/p/Bu1l
Hoto: AP

Kasar Burtaniya dai tuni tace,ta sadaukar da kanta ga taimakon nahiyar Afrika,wanda batun taimakawa nahiyar ce Burtaniya ta bada fifiko akai wajen yekuwarta ta samun shugabancin kungiyar kasashe 8 masu arzikin masanaantu a duniya.

Daya kuma daga cikin muhimman batutuwa sun hada da harkar man fetur da iskar gas,manyan batutuwa da kasashen yammacin duniya suka fi bada fifiko akai domin kokarinsu na rage dogaro akan yankin gabas ta tsakiya.

Ana sa ran Jack Straw zai kai ziyara yankin Naija Delta,inda yan gani kashe ni,dake yankin mai arzikin man fetur,suke tada hankulan jamaa musamman barazana da sukeyiwa tsaron yankin,bayan sace wasu turawa maaikatan wani kanfanin hako mai da sukayi kwanan nan.

Kasar Burtaniya dai ta dauki Najeriya,wadda tayiwa mulkin mallaka,kuma kasa ta 8 a jerin kasashe da suka fita da man fetur a duniya,a matsayin wata kasa da ka iya taka muhimmaiyar rawa a nahiya mafi talauci a duniya.

Wani jamiin kasar Burtaniya ya fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa,Burtaniya tana goyon bayan shirye shiryen shugaba Obasanjo tare kuma da rawa da Najeriya take takawa a nahiyar Afrika,musamman a fannonin zaman lafiya,tsaro da tabbatar da kyakkyawar shugabanci.

Jamiin na Burtaniya yace,Burtaniya tana ganin cewa idan komai ya daidaita a Najeriya,to dukkan nahiyar Afrika zata daidaita.

Abinda sakataren na Burtaniya kuma yake son Obasanjo yayi shine,nuna kyakyawar misali ga sauran kasashen Afrika,yayinda ake ci gaba da korafe korafe game da batun tazarce a Najeriya.

Shugabannin kasashen Afrika da dama ciki har da shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda sun nemi kara waadin mulkinsu.

Amma shugaban Najeriya,Obasanjo yayi shiru game da rade radin,na ko zai yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima,ta yadda zai samu damar zarcewa a 2007.

Wannan batu ne da Burtaniya take son samun tabbaci a kansa daga shugaban na Najeriya,tare da mika bukatar kada a kawo sauyi cikin kundin,yayin wannan ziyara.

Wasu jamian diplomasiya sun baiyana tsoron cewa,idan idan har Obasanjo ya nemi zarcewa a 2007,akwai yiwuwar barkewar rikici a kasar.

Kasar Burtaniya dai ta yanke dukkan taimako zuwa kasashen Uganda da Habasha,tana mai zarginsu da gaza gudanar da harkokin demokradiya yadda suka kamata.

Wata jamia a cibiyar tsara manufofin wajen Burtaniya,Josephine Osikana,tace tana ganin yan Najeriya da dama zasuyi maraba da martani mai karfi daga Jack Straw game da batun tazarce.

Tace,Obasanjo dattijo ne da ake kauna a wajen nahiyar,amma baa mutunta shi yadda ya kamata a Najeriya,ganin cewa ya gagara biyan bukataun wadanda suka zabe shi.

Obasanjo dai ya kirkiro na shiryukan gyare gyaren tattalin arziki,ya kuma dauki matakan magance cin hanci da rashawa,sai dai masu sukan alamuransa suna ganin cewa,ya fi daukar wadannan matakan ne akan abokan adawarsa.