1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Jacob Zuma a Najeriya da nufin dinke baraka

Ubale Musa/ MNAMarch 7, 2016

Daidaita sahu tsakanin Afirka ta Kudu da tarayyar Najeriya bayan tsawon lokaci na takun saka tsakanin manyan kasashen biyu na Afirka.

https://p.dw.com/p/1I8qb
Äthiopien Gipfel Afrikanische Union - Muhammadu Buhari & Jacob Zuma
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Kama daga hari irin na kyamar baki ya zuwa cafke kudade na haramun dai ta yi baki ta yi kuma muni a tsakanin tarrayar Najeriya da takwararta ta Afrika ta Kudu da ke zaman manya a cikin nahiyar Afrika a halin yanzu.

To sai dai kuma sauyi na shugabanci a cikin tarrayar Najeriya game da taku na rawa sannu a hankali na neman sauyin lamura a tsakanin giwayen biyu da ke bukatar juna yanzu.

A wannan Talata ne dai Shugaban kasar ta AfriKa ta Kudu Jacob Zuma zai kasance a Abuja da nufin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da za ta kalle shi hadin gemu da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar da kuma jawabi ga majalisun tarrayar kasar biyu.

Ziyarar na da burin dinke baraka

Ana dai kallon ziyarar da ko bayan jami'ai na gwamnati ta kunshi manya na 'yan kasuwar AfriKa ta Kudu da dama dai a matsayin wani kokari na dinkin barakar da ta faro tun bayan koro wasu 'yan Najeriya da Afrika ta Kudun ta ce sun kai ga shiga kasarta babu cikakken izini.

Mosambik Friedensmarsch in Maputo
Zanga-zangar adawa da kyamar bakiHoto: DW/L. Matias

Ko bayan hari na kyamar baki dai Afrika ta Kudun na kuma korafi na cin zarafin wasu 'ya'yanta 84 da suka rasa ransu a wata Coci a Legas amma kuma aka rike gawarwakinsu har na tsawon watanni tara.

Ko bayan nan dai mai masaukin bakin ta kakaba tara kan babban kamfanin sadarwar kasar na MTN da ta zarga da karya ka'idojin kasar da kuma ta ce ya biya Naira miliyan dubu 780 da ke zaman tara mafi girma a tarihin kasar.

To sai dai kuma a fadar Geoffrey Onyeama da ke zaman ministan harkokin wajen Najeriya banbanci na kasashen biyu bai isa sasu nise da junansu na lokaci mai nisa ba.

"Akwai abubuwa da yawa da ke kafafen labarai game da 'yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu. Amma muna kokarin ganin wannan ba zai dusashe dangantaka a tsakanin kasashen biyu ba. Kuma har ila yau ziyarar na da muhimmanci saboda za ta bamu damar kallon tsaf na dalilan matsalolin da kuma hanyar samo mafita. Kuma al'ummar kasashen biyu na iya kallon kusancin da ke tsakanin kasashen biyu, abun kuma da zai iya kara sanyaya dar-dar din da ke iya faruwa a wani matakin."

Sauyi a harkar kera makamai da horas da jami'an tsaro

Tuni dai alamar sauyin ta fara tare da ministan harkokin tsaron kasar ta Afrika ta Kudu Nosiviwe Mapisa-Nqakula ziyarar ban girma ga takwaranta na tarrayar Najeriya a Abuja in da kuma bangarorin biyu suka nuna alamar aiki tare da nufin taimaka wa tarrayar Najeriyar wajen kera makamai a fadar Janar Mansur Mohammed Dan-Ali da ke zaman ministan tsaron tarrayar Najeriya.

Südafrika Verteidigungsminister Nosiviwe Mapisa-Nqakula
Ministar tsaron Afirka ta Kudu Nosiviwe Mapisa-NqakulaHoto: S. de Sakutin/AFP/Getty Images

Ita ma dai ministar ta tsaro ta ce ta zo Najeriya ne da nufin sanin irin yadda taimako a tsakanin juna zai habaka.

"Daga tattaunawar da muka yi da minista da kuma wadda ta gudana tsakanin manyan hafsoshinmu, ina sane cewar sun kalli hadin kai ta wajen horarwa, da kuma bincike da habakawa. Mun nuna sha'awarmu sosai kan wannan, sannan kuma da musayar matsakaitan hafsoshi. Sannan kuma muna fatan samun dangantaka mai karfi a tsakanin masana'antar kera makaman tarrayar Najeriya da kuma 'yar uwarta ta Afrika ta Kudu."

Ana dai sa ran shugabannin biyu za su yi jawabi na hadin gwiwa ga wani taron manyan 'yan kasuwar kasashen biyu da za su gana a Abuja, kafin daga baya ya bar kasar a ranar Laraba.