1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR JAMIAN EU A SUDAN.

October 13, 2004
https://p.dw.com/p/Bvfa
Bernard Bot,Ministan harkokin wajen Holland.
Bernard Bot,Ministan harkokin wajen Holland.Hoto: AP

Kungiyar gamayyar Turai EU,ta gargadi gwamnatin Sudan danganeda yiwuwar kakaba mata takunkumi ,idan har ta gaza wajen inganta rayuwar mazauna Lardin Darfur nan da watanni biyu.

Ministan harkokin wajen kasar Holland,wanda kasarce ke rike da zagayen shugabancin kungiyar gamayyar Turan Bernard Bot,yayi maraba da yadda gwamnatin Khartum ta amince da a tura ayarin masu lura kimanin 4,000,daga sauran kasashen Afrika,tare da alkawarin hadin kai da MDD wajen binciken ko rikicin na Darfur ya kunshi kisan kare dangi.

Sai dai ya dada jaddada cewa akwai bukatr dada matsa kaimi wajen kwance damarar mayakan,gurfanar da wadanda suka tozartawa mutane gaban hukuma,tare da dawar da kimanin mutane million 1 da Rabi da suka tsere,zuwa kauyukansu.

Mr Bot ya fadawa manema labaru bayan ganawa da ministan harkokin wajen Sudan Mustapha Ismail cewa, babu wani tudun da aka cimma dangane da kare rayukan fararen fata a Lardin na Darfur ya zuwa yanzu.

Jagoran kungiyar gammayar turan yace idan har nan da watanni biyu masu zuwa gwamnatin Sudan din batayi wani abun azo a gani dangane da halinda alummar wannan lardi ke ciki ba,to kungiyar ta EU bata da wani zabi face kakaba mata takunkumi na tattalin arziki.Kazalika matsin lamba daya hadar da kakabawa kungiyoyin yan tawayen yankin shima,zai kasance wajibi,inji shi.

Wannan rikicin dai ya taso ne tsakanin makiyaya Larabawa da bakakensu manoma,a dangane da karancin albarkatu a Lardin na Darfur,dake kann iyakar tchadi da sudan ta yammaci.a Bara ne yan adawan suka saba makamai ,inda suka zargin gwamnatin Khartum da nuna musu wariya,tare da amfani da mayakan Larabawan da akafi sani da suna Janjaweed ,wajen sata tare da kone kauyukan bakaken larabawan,banda kisan gilla da suke musu.

Gwamnatin sudan dindai ta karyata wannan zargi,tare da karin hasken cewa tana iyakar kokarinta wajen samarda zaman lafiya a wannan yanki.
Mdd data bayyana rikicin na Darfur da kasancewa mafi munin irinsa,ta kiyasta cewa akalla mutane dubu 50 suka rasa rayukansu.

Mr Bot yace gwamnatin Sudan din ta nemi agajin tsaro daga waje,inda yayi kira da kungiyar gamayyar Afrika data gaggauta tura ayarin Sojojinta datayi alkawri.Ya kara dacewa EU zata taimaka da kudi da wasu abubuwanda da dakarun Afrika zasu bukaci amfani dasu a Sudan din.

Zainab Mohammed.