1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ziyarar jamiin kula da yan gudun hijiran mdd a Liberia

Zainab A MohammedJune 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6W

A yau ne shugaban hukumar lura day an gudun hijira ta Mdd Antonio Gutterres,zai isa kasar Liberia domin ganewa idanunsa halin da ake ciki ,dangane da komowar yan kasar dake gudun hijira a kasashe dake makwabtaka da ita.Sanar daga hukumar kula day an gudun hijiran na nuni dacewa,jamiin zai yi laakari da yadda shirin komar day an gudun hijiran ke gudana .Ana saran Mr Gutteres zai gudanar da bukin ranar gudun hijira da mdd ke daukan nauyin gudanar akowace shekara a Liberian,inda zai marabci ayarin yan gudun hijira dake komowa gida daka kasar Saleon,watanni 6 bayan nada zababbiyar gwamnatin democradiyya,sakamakon kawo karshen yakin basasa daya dauki shekaru 14 yana gudana a wannan kasa dake yammacin Afrika.Akan gudanar da bukin wannan rana ne domin laakari da halin day an gudun hijira ke ciki a sassa daban daban na duniya.Anasaran Jamiin na Mdd zai taryi yan gudun hijiran a bakin kogin Bo,kana zai rakasu birnin Monrovia.

Kimanin yan kasar ta Liberia dubu 270 suka komo gida daga gudun hijira tun daga watan yulin 2003,kawo yanzu.