1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Joe Biden a Gabas Ta Tsakiya.

March 10, 2010

Amirka zata tallafawa Falasɗinawa samun 'yantacciyar ƙasarsu.

https://p.dw.com/p/MPDu
Joe Biden da Mahmud AbbasHoto: AP

Mataimakin shugaban ƙasar Amirka Joe Biden, ya bayyana cewar, Falasɗinawa sun cancanci samun 'yantacciyar ƙasa - ta kansu, kuma mai ta'asiri. Mr Joe Biden, ya kuma tabbatarwa Falasɗinawa cewar, Amirka zata ci gaba da basu goyon baya wajen fafutukar cimma wannan burin. Furucin na Mr Biden, ya zo ne bayan da Isra'ila ta yi shelar faɗaɗa gine gine a matsugunan yahudawa a yankunan Falasɗinawa dake gabashin birnin Jerusalem. Sanarwar da Isra'ila ta bayar ne dai ta mamaye ziyarar da Biden ke yi a yankin gabas ta tsakiya, a ƙaƙoarin farfaɗo da tattaunawar samar da zaman lafiya a tsakanin sassan biyu. Sai dai kuma Isra'ila ta nemi afuwa bisa lokacin data zaɓa domin yin sanarwar, kasancewar wasu na ganin hakan a matsayin wulaƙanci ne ga mataimakin shugaban na Amirka, amma ta ce babu ja - da baya game da shirin faɗaɗa gine ginen. Ƙungiyar tarayyar Turai, da kuma Sakataren kula da harkokin wajen Birtaniya, David Milliband, sun buƙaci Isra'ila ta sauya matsayinta game da wannan sanarwar, domin a cewar su hakan zai janyo ƙafar ungulu ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Abdullahi Tanko Bala