1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ziyarar kwanaki uku da Mr Egeland keyi a Ivory Coast

February 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7s

A wani lokaci ne a nan gaba kadan a yau ake sa ran shugaban hukumar bayar da tallafin gaggawa na Mdd, wato Mr Jan Egeland zai kai ziyara izuwa garin Guiglo dake yammacin kasar Koddebuwa.

Kafin dai wannan ziyara, a jiya Mr Egeland ya bukaci gwamnatin kasar data dauki matakin kwancewa yan tawayen kasar damara, a

hannu daya kuma da zakulo wadanda suka kaiwa jami´an hukumar da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya hari a watan daya gabata don hukunta su.

Mr Egeland , wanda ya isa kasar ta Kuddebuwa a ranar talata, na gudanar da ziyarar aiki ne ta tsawon kwanaki uku.

A wata sabuwa kuma Mdd ta aike da karin sojin kiyaye zaman lafiya zambar 200 izuwa kasar don bunkasa harkokin tsaro ga kayayyakin majalisar dake kasar ta Ivory Coast.