1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel a yankin Gulf

May 26, 2010

Saudiya ta tabbatar da goyon bayan ƙasashen yamma, a taƙaddamarsu da ƙasar Iran

https://p.dw.com/p/NXxy
Merkel a ƙasashen larabawaHoto: picture-alliance/dpa

A ci gaba da ziyar da take yi a gabas ta tsakiya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta taɓo batuwa da dama waɗanda suka haɗa da batun samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palsɗinawa da dama batun da yashafi nukilyar ƙasar Iran.

Da ta ke ganawa da jam'an ƙasar Saudiya, shugabar gwamnatin Jamus, ta saurari irin koke koken da mahukuntan ƙasa mai tsarki ke da su kan yadda Tarayyar Turai take sanyi jiki bisa matsawa Isra'ila, a kan abinda yashafi tsakanin su da Palasɗinawa. Ƙasar Jamus dai ta taɓa tura masu ayyukan kiyaye zaman lafiya na farar hula a yankin Palsɗinu, don haka Sarki Abdullah ya roƙi Merkel ta yi anfani da matsayin da Jamus ke da shi a Tarayyar Turai, don ganin sun haɗu da Amirkawa wajen warware rikishin gabas ta tsakiya, wanda Sarkin ya kwatanta da wani abun takaici.

Shugabar gwamnatin Jamus dake tafe da Jamsuwa 'yan kasuwa a tawaggar ta, sun sanya hannu da 'yan kasuwan Saudiya bisa fannonin kasuwanci masu yawa.

Saudi Arabiya ƙasashe mai ƙarfin faɗa aji ta fannin tattalin arziki a yankin Gulf, kuma Jamus tana da damar anfani da hulɗar da take tsakaninmu, don sayar da hajojin mu. Bugu da ƙari a ziyar da na kai a jami'ar sarki Abdallah, na ga cewa Saudiya tana ciki shirin tunkarar sabon zamani"

A kan abinda ya shafi ƙasar Iran, Merkel tace ta samu tabbaci daga sarki Abdullah, wanda yace zai yi anfani da ɗasawar da yake yi da ƙasashen Rasha da China, don ganin sun amince a ladabtar da Iran, har sai ta fito a fili ta bayyana manurafta na samun ukiliya.

Ƙasar Saudi Arabiya dai ƙasashe da ake yiwa kallon rashin baiwa mata yancinsu, sai dai Merkel ta bayyana gamsuwarta bisa irin sauyin da ta gani a fanni baiwa mata yanci.

Eh na yi imanin wannan bangaren wani abune da ake son kyautatawa, to amma da sannu-sannu ake samun biyan buƙata, kuma akwai fata na gari. Misali lokacin da muka ziyarci jam'ar sarki Abdullah, munga mata suna ɗaukar karatu yadda yakamata. Wannan abune da ada a Saudiya ba mai saɓuwa bane"

Merkel ta kuma taɓo batun tattalin arzikin duniya wanda yake fama da mugun zazzaɓi, kana tace tana fatan samun goyon bayan Saudiya, a taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G20, wanda za'a gudanar a ƙasar Kanada. Jamus dai tana son saka wani haraji kan hada hadar kuɗi na duniya, abinda tace Saudiya tana da ribar da za ta samu idan hakan ta samu karɓuwa, a matsayin ta na ƙasar da ke da azikin ɗanyen mai. Shugabar gwamnatin Jamus a yanzu ta nufi ƙasar Qatar, cikin ziyar kwana huɗu a yankin Gulf da ta kai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu tijjani Lawal