1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Indonesiya A Berlin

January 13, 2005

A yau da sanyin safiya ministan harkokin wajen Indonesiya ya sadu da takwaransa na Jamus domin tattauna maganar taimakon jinkai ga lardin Aceh da bala'in tsunami ya rutsa da si

https://p.dw.com/p/Bvdf
Fischer da Wirajuda
Fischer da WirajudaHoto: AP

Jamus dai a shirye take ta ci gaba da rufa wa kasar Indonesiya baya har ya zuwa wani lokaci mai tsawo nan gaba. Wannan bayanin an ji shi ne daga bakin ministan harkokin wajen kasar Joschka Fischer a yau alhamis da sanyin safiya, bayan da suka gana da takwaransa na Indonesiya Hassan Virayuda domin tattauna irin taimakon da za a iya ba wa mutanen da masifar tsunami ta rutsa da su a lardin Aceh na kasar Indonesiya. Fischer ya ce muhimmin abin dake akwai shi ne taimakon ya isa ga mabukata. Ministan harkokin wajen na Jamus ya bayyanar a fili cewar dorewar taimakon na Jamus ya danganta ne da rawar da gwamnatin Indonesiya zata taka bisa manufa. Fischer ya ce:

Zamu ci gaba da amfani da kafofin taimakon da muka tanadar, kamar dai asibitin jirgin ruwan nan na sojan Jamus da dai sauran kayan taimakon da muka tanadar, wadanda za a iya ci gaba da amfani dasu matsawar da gwamnatin Indonesiya ke bukata.

A baya ga jami’an taimako farar fula Jamus ta tura sojojinta domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan taimakon jinkai a lardin Aceh. A jiya laraba mataimakin shugaban kasar Indonesiya Yusuf Kalla yayi nuni da cewar wajibi ne dukkan sojojin ketare su tashi daga lardin da bala’in ya rutsa da shi a cikin watanni uku masu zuwa. To sai dai a nasa bangaren ministan harkokin wajen Indonesiya Hassan Virayuda yayi gyara ga wannan bayanin, inda ya ce zaman jami’an taimakon Ya-Allah farar fula ne ko soja, ya danganta ne da irin ci gaban da aka samu akan manufa. Gwamnatinsa dai na sa ran cewar taimakon na gaggawa zai dauki shekara daya ana gudanar da shi. Idan har matakan taimakon sun tafi daidai yadda ya kamata, nan da watanni uku masu zuwa ana iya janye dakarun soja daga wadannan matakai. Abu daya da Indonesiya ba zata iya yi watsi da shi ba shi ne taimakon kudi, wanda take bukata ruwa a jallo. A sakamakon haka ne gamayyar kasashen Paris Club su 19 suka yi wa kasar indonesiyan da sauran kasashen da tsautsayin ya rutsa dasu tayi dage wada’in biyan basussukan dake kansu har tsawon shekara daya. Bisa ta bakin Hassan Vraduya dai gwamnatin Indonesiya na bitar wannan tayi da aka gabatar kafin ta mayar da martanin da ya dace bisa manufa. Kasar dai ta kan biya abin da ya kai dala miliyan dubu 10 domin mayar da basussuka na sama da dala miliyan dubu dari tare da kudaden ruwa dake kanta.