1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Jamus A Washington

May 12, 2004

A lokacin da suka gana da takwaransa sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell, ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya ce wajibi ne Amurka dauki matakan da suka dace akan sojojinta dake da laifin azabtar da fursinoni a kasar Iraki

https://p.dw.com/p/Bvji
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer da takwaransa Colin Powell
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer da takwaransa Colin PowellHoto: AP

A hakika dai mutum ba ya kin ta mutane. Ita kanta kasar Amurka duk da kasancewar ta fi kowace kasa a duniyar nan karfin soja, amma tana bukatar kawaye da abokan hulda, musamman ma ganin yadda martabarta ke dada zubewa a idanun jama’a a dukkan sassa na duniya sakamakon tabargazar nan ta azabtar da fursinoni a kasar Iraki. Fischer, wanda ya kai ziyara birnin Washington domin nuna wa Amurka zumunci a daidai wannan lokaci da take fama da hali na kaka-nika-yi, bai yi wata-wata ba wajen yin kira ga shuagabannin babbar daular ta duniya da su dauki nagartattun matakai da suka dace domin warkar da wannan mummunan tabo na tabargazar azabtar da fursinoni da sojojin kasar suka yi, ba gaira ba dalili, a kasar Iraki domin ta haka ne kawai za a rika ganinta da mutunci a duniyar baki daya. Ziyarar ta Fischer tana da muhimmanci saboda kokari da gwamnati a birnin Berlin take yi na taka wata rawa ta mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya. To sai dai kuma wannan mataki na diplomasiyya ba zai cimma nasara ba sai fa idan kasashen Larabawa sun amince da wannan rawa da Jamus ke so ta taka. A dai halin da muke ciki yanzu, kasar Amurka, a sakamakon wannan abin kunya da sojojinta suka caba a kurkukun Abu Ghoraib a kasar Iraki, ta tsayar da shawarar sake shiga zauren shawarwarin sulhu tare da Palasdinawa a kokarin sake dawowa da martabarta da ta zube a idanun illahirin al’umar Larabawa a Yankin Gabas ta Tsakiya. Shi kuma ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya lura da haka a saboda shi yayi amfani da wannan dama wajen shirya ganawa tsakanin Condoleeza Rice da Ahmad Kurei’i a birnin Berlin. Shekara daya bayan sabanin da aka sha fama da shi tsakanin Amurka da Jamus akan yakin Iraki, ga alamu fadar mulki ta White House, a yanzu ta ankara da muhimmancin manufofin diplomasiyyar Jamus, musamman ma ganin cewar kasar Birtaniya, babbar kawar Amurka wajen yakar Iraki, ita ma tana da rabonta na alhakin azabtar da fursinoni da keta hakkin dan-Adam a wannan kasa. Muhimmin abin dake akwai a yanzun shi ne a samu hadin kai tsakanin Amurka da kwamitin sulhu na MDD wajen ba wa gwamnatin rikon kwaryar da za a nada a Iraki wani nagartaccen fasalin da zai taimaka mata ta samu ikon tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a kasar. Wajibi ne Amurka ta kawo sauyi ga rawar da sojojinta ke takawa a Iraki. A maimakon ci gaba da zama wasu sojoji na mamaye kamata yayi su nemi hadin kai da kusantar juna da al’umar Iraki ta haka ne kawai za a samu nasara wajen sake gina kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita. Tabargazar azabtar da fursinonin dai ta kara gurbata yanayin alakar Irakawa da Amurkawa.