1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar ministan harkokin wajen Jamus Jung a Washington

December 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvFi

Sabon ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung wanda a halin yanzu yake wata ziyarar aiki a birnin Washington ya yi kira da a inganta huldar dangantaku tsakanin Jamus da Amirka don magance rashin jituwar da ta taso akan yakin kasar Iraqi. Bayan ya tattauna da takwaransa na Amirka Donald Rumsfeld, Jung ya ce ya yi murnar cewa Amirka ta amince da shawarar da Jamus ta yanke a shekara ta 2003 na kin tura dakarun Jamus din zuwa Iraqi. Jung ya jaddada cewar dakarun Jamus da ke aikin kiyaye zaman lafiya karkashin rundunar ISAF da kungiyar tsaron NATO ta girke a Afghanistan ba zasu shiga cikin aiki nan da ake yiwa lakabi da jurewa ´yanci ba, wato Enduring Freedom, wanda wani bangare ne na yaki da ta´addanci da Amirka ke yi a Afghanistan.