1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar ministan harkokin wajen Najeriya a DW

Umaru AliyuJune 15, 2016

Batun 'yan Najeriya da ke zama bakin haure a Turai da yankin Niger Delta da yaki da cin hanci da rashawa suna daga cikin al'amuran da ministan ya tabo lokacin hira da sashen Ingilishi a Bonn.

https://p.dw.com/p/1J6hi
GMF nigerianischer Außenminister Geoffrey Onyeama und Peter Limbourg
Minista Goffrey Onyeama da darektan DW, Peter LimbourgHoto: DW/U. Shehu

Ranar Talata, ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya kawo ziyara a tashar DW, inda bayan ganawar da ya yi da shugaban tashar, Peter Limbourg, da halartar zauren taron 'yan jaridun duniya, wato Global Media Forum a Bonn, ya yada zango a sashen Hausa, inda ya shaidar da yadda ake tafiyar da aiyukan yada labarai. Daga baya, ministan ya yi hira da sashen Ingilishi, inda ya baiyana wasu daga cikin manufofin gwamnatin Najeriya kan al'amura da dama.

Da farko dai ministan harkokin wajen na Najeriya ya yi magana kan batun kwararar 'yan Najeriya yawancinsu bakin haure daga kasashen Afirka zuwa Turai. Najeriya tana daya daga cikin kasashen da Kungiyar Hadin Kan Turai ta ce za ta nemi hadin kai da su a wani shiri na rage kwararar dimbin 'yan Afirka zuwa Turai, inda da dama suke mutuwa kan hanya ko dai a teku ko a hamada. To ko shin me Jamus ta ce za ta yi wa Najeriya yadda za ta hana 'yan Najeriyar fitowa zuwa Turai? Ministan ya ce shi a ra'ayinsa, Jamus ba tana hana 'yan Najeriya zuwa cikin kasar ba ne. Abin da yake matsala sh ine neman zuwa Jamus din ta barayin hanyoyi.

Ya ce "babbar matsalar dai ita ce yadda za mu daidaita a game da mayar da 'yan Najeriya da suka shigo ba tare da izini ba, wato yadda za mu sami wata hanya ta bai daya ta maido mana da wadannan 'yan Najeriya da suka zama bakin haure a nan. Wannan shi ne abin da muke dubawa. Sai dai wani abin da ke kawo mana cikas shi ne rashin sanin ainihin yawa ko kuma su wanene 'yan Najeriya, saboda irin wadannan mutane sau tari sukan lalata takardunsu, ko ma su ki yarda da kasarsu ta asali."

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya yi magana a game da matakan da gwamnatin Najeriya take dauka domin rage sha'awar 'yan Najeriya, musamman matasa masu son zuwa Turai.

Geoffrey Onyeama Nigeria und Claus Stäcker
Minista Onyeama da shugaban sashen Afirka Claus StäckerHoto: DW/T.Mösch

Ya ce "wannan al'amari ne da ke da dangantaka da yadda ake mulkin jama'a da kuma hangensu ga samun wata makoma mai haske a gida. Abin dai ya shafi matsayin tattalin arziki ne da batun tsaro. Hakan shi ya sanya wannan gwamnati ta maida hankalinta kan dalilan da ke jawo matasan su nemi kaura zuwa Turai, musamman 'yan Najeriya da ke shirin daukar matakai masu hadari domin zuwa Turai, inda da yawa daga cikinsu suke gamuwa da karshensu, ko dai a tekun Bahar Rum ko a hamada."

Ministan ya kuma tabo batun rikicin da ke gudana a yankin Niger Delta, yankin da ke da muhimmanci ga tattalin arzikin kasar, amma a yanzu yake fuskantar barazana daga kungiyoyi na 'yan takife.

Ya ce "a da can an cimma wata matsaya da kungiyoyin 'yan takife dabam-dabam domin shigar da su a batun kare wadannan hanyoyi na jigilar man fetur, tare da biyansu kudi mai yawa, to amma yanzu saboda matsin tattalin arziki wannan gwamnati ba ta da wannan kudi da za ta biya. Saboda haka ne yanzu ake kokarin ganin yadda za a shawo kan al'amarin. Ina fata haka za ta cimma ruwa, domin kuwa halin da ake ciki a Niger Delta yanzu ba abu ne mai kyau ga al'ummar yankin ba, ko ga su kansu masu tada kayar bayan ko kuma ga gwamnatin tarayya."

Minista Onyeama ya kuma musunta zargin cewar wai yakin da gwamnatin Najeriya take yi yanzu kan cin rashawa, musaman ya shafi jami'an da suka rike mulki ne a tsohuwar gwamnati kawai, inda ya ce abin da gwamnatin yanzu ta damu da shi shi ne wadanda suka kwashe dukiyar kasar ta hanyoyi na haramun su dawo da ita. Ba mutane ake farauta ba amma dukiyar kasa da suka kwashe kawai ake so su dawo da ita. A game da zargin cewar wai gwamnatin Najeriya tana farautar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ministan Onyeama ya ce babu gaskiya a hakan. Tsohon shugaban ma yana daga cikin wadanda gwamnatin take takama da su, kuma Jonathan mutum ne da mutuncinsa ya daukaka saboda yadda ya mika wa gwamnatin da ke ci a yanzu mulki bayan ya sha kaye a zabe.

GMF nigerianischer Außenminister Geoffrey Onyeama und Thomas Mösch
Minista Onyeama da shugaban sashen Hausa Thomas MöschHoto: DW/U. Shehu