1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR MINISTAN TSARON JAMUS PETER STRUCK A KUNDUS.

Yahaya AhmedFebruary 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvm9
Yayin da sojojin Jamus suka isa a lardin Kundus a arewacin Afghanistan dai, jama'ar yankin sun yi musu kyakyawar marhaba. Amma kai tsaye za a iya ganin cewa ba sa cikin kwanciyar hankali. Ban da dai birnin Kabul da kewayensa, inda tashe-tashen hankulla ke da dan sauki, a ko'ina a kasar ta Afghanistan, jama'a na zaune ne cikin shirin ko ta kwana. A ko yaushe rikici zai iya barkewa tsakanin kungiyoyin da ke hamayya da juna, kuma nan da nan sai ka ga sun fara bude wa juna wuta. Babban mai fada a ji a yankin Kundus din dai, shi ne ministan tsaron Afghanistan, Fahim, wanda yake da mayakansa daban, ban da dakarun kasar da ke karkashin ma'aikatarsa. Su wadannan mayakan ne kuwa, ke sintiri a duk muhimman biranen yankin. Shugaban wannan rukunin, Mohammed Daud, ya bayyana cewa, a lokaci daya zai iya tara dakaru dubu 30, idan bukata ta kama. Ashe kuwa sojojin Jamus dari 2 da 30 da aka girke a yankin, ba su da ta fada sai dai sun sami amincewar shi Daud din. A zayyane dai, sojojin na Jamus, ba su da damar yin katsalandan a harkokin cikin gida na wannan yankin. Aikinsu ne kare ma'aikatan da ke ayyukan sake gina kasar a wanna jihar. Amma duk da haka, kamata ya yi su yi taka tsantsan a duk wani matakin da za su dauka, don kada a sami sabani tsakaninsu da rundunar Mohammed Daud. A bangare daya kuma, bai kamata shugabannin dakarun Jamus da ke girke a Kundus din, su bai wa mayakan Daud damar yin amfani da su ba, wajen fatattakar abokan hamayyarsu. A ziyarar da ministan tsaron Jamus peter Sstruck ya kai a jihar dai, ya sami ganawa da shi Daud, inda kuma suka tatttauna batun kayyade aikin da dakarun Jamus za su yi a yankin. Wasu rahotanni sun ce, ministan ya yi watsi da bukatar da Daud din ya gabatar masa, na neman taimakon dakarun Jamus, wajen yakan masu harkar miyagun kwayoyi. A nan dai wani rikici ne da ya barke tsakanin kungiyoyi masu hamayya da juna a kan harkar miyagun kwayoyin. A cikin wadannan kungiyoyin kuwa, har da na shi Daud din. Wato ke nan, idan dakarun Jamus suka shiga cikin rikicin, su ke nan za su zamo abokan gaba ga sauran kungiyoyin, wadanda babu shakka za su yi ta yakansu, abin da kuma zai kara tabarbare al'amura. A halin yanzu dai, babu wani tashin hankali a yankin na Kundus. Amma idan aka sami hauhawar tsamari tsakanin abokan hamayya na yankin, har ya kai ga barkewar tashe-tashen hankulla, to babu shakka, ko wane irin mataki sojojin Jamus din suka dauka na zaman `yan ba ruwanmu, wasu kungiyoyin za su yunkuri kai musu hari. Aikin da dakarun Jamus din ke yi na kare ma'aikatan kasa da kasa, a yankin na kundus yana da muhimmanci kwarai. Amma Jamusawa da yawa na ganin cewa, wannan kadai bai hujjanta girke dakarun a can ba, saboda za su huskanci wani babban kalubale da kuma kasada ta asarar rayukansu, idan al'amura suka tabarbare har ya kai ga fafatawa tsakanin kungiyoyin da ke yankin, wadanda kuma suka ci damaru kicin-kicin.