1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

070410 Westerwelle Niebel Afrika

April 7, 2010

Rangadin ministocin harkokin waje da raya ƙasashe na Jamus, a Afirka

https://p.dw.com/p/Mpfp
Guido Wsterwelle, da Dirk Niebel.Hoto: AP

A karon farko, ministocin harkokin waje da na raya ƙasashe masu tasowa, wato Guido Westerwelle da Dirk Niebel , sun tashi tare domin yin rangadi a Afirka. A ranar Lahadi ne kuma za su kawo ƙarshen wannan ziyara tasu da yin rangadin ƙasashen Tanzaniya, Afirka ta Kudu da kuma Djibouti. Ko kafin gudanar da zaɓen majalisar dokoki a Jamus ne jam'iyyar FDP ta miƙa buƙatar wargaza ma'aikatar haɗin-gwiwar tattalin arziƙi da raya ƙasashe masu tasowa.To amma kuma wannan batu a yanzu ba a ɗaukarsa da muhimmaci. A ra'ayin Dirk Niebel,. ministan haɗin-gwiwar tattalin arzƙi da raya ƙasashe masu tasowa dai wannan buƙata martani ne da ke nuni da saɓanin da ake yawaita samu tsakanin ma'aikatar harkokin wajen da ma'aikatar raya ƙasashe masu tasowa.Dirk Niebel ya nanata cewa an samu ci gaba sosai tun bayan zaɓen majalisar dokoki:Ya ce " Bai dace ba a ce ministan harkokin wajen ya kai ziyara a ranar Litinin a babban birnin wata kasa kafin ministan raya kasashe ya kai tasa ziyarar a ranar Alhamis, kuma hakan wani abu ne da ke nuni da saɓanin manufa da ake samu tsakanin su biyun. Dalilin kenan da ya sa na miƙa wannan buƙata ta siyasa inda muke tabbatar da cewa baki zai zo ɗaya game da matakan da muke ɗauka a manufofinmu na ƙetare. A haƙiƙa samar da ma'aikatu biyiu a wuri ɗaya mataki ne da zai samar da ci-gaban aikin haɗin-gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa.

A 'yan kwanaki da suka biyo baya ministocin biyu suka tashi a lokaci guda domin kai ziyara a Afirka, da yake ya bai zamo wajibi su sauya jadawalinsu don daɗaɗa wa juna ba. Abin da ministocin biyu ke buƙatar gwadawa yayin wannan ziyara tasu shi ne sasantwa a maimakon yin takara tsakaninsu. Marina Schuster, na zaman 'yar majalisa ta jam'iyyar FDP. Tana mai ra'ayin cewa wannan shi ne abin da ya kamata a yi amfani da shi domin cimma manufofin Jamus akan Afirka:Ta ce "Muna buƙatar nuna wa duniya cewar akwai buƙatu da dama da muke muradin cimma a Afirka. Kuma so muke mu yi haɗin-gwiwa domin cimma buƙatunmu a wannan wuri. Na yi imanin cewar wannan dai wata muhimmiyar alama ce"

NO FLAS Dirk Niebel in Afrika
Dirk Niebel yayin wata ziyara a Afirka.Hoto: picture alliance/ dpa

A dai manufofinta akan Afirka, Jamus ta fi mai da hankali ne ga buƙatun gaggawa. Saboda haka ana buƙatar yin haɗin-gwiwa tsakanni ma'aikatu daban daban domin samar da ƙarin kuɗin da ake buƙata wajen ba da taimakon raya ƙasashe masu tasowa. Sai dai babban kuskure da Jamus ta tafka a can baya shi ne rashin sanin inda ya dace ta ba da fifiko tsakanin manufarta ta raya ƙasashe masu tasowa da kuma ba da taimakon jinƙai na gaggawa.

05.04.2010 DW-TV GLOBAL 3000 Klima Tansania 3
Mata masu karbar agaji a Tanzaniya.Hoto: DW-TV

Christian von Soest ƙwararren masani ne akan Afirka da ke aiki a makarantar nazarce-nazarcen Afirka ta GIGA. A nasa ra'ayin dai a bayyane yake cewa kowa ya san inda Jamus ta nufa domin cimma buƙatunta a Afirka.Ya ce "A fannin manufofinmu na ƙetare da kuma tsaro akwai ƙasashen da dama na Afirka da ba sai an mai da hankali akansu ba. Magana ta biyu kuma ita ce Jamus kasa ce da ke sayar da hajojinta ga ƙasashen ƙetare inda hakan ke ma'anar cewa muna buƙatar samun kyakyawar dangantaka ta tattalin arziƙi . A Afirka akwai jerin ƙasashen da suka samu ci gaba mai ma'ana."

A yayin ziyarar tasu ministocin biyu za su yi rangadi ne kama daga kasar Tanzaniya da sauran ƙasashe da ke aikin haɗin-gwiwa da Jamus da suka haɗa da Afirka ta Kudu.

Mawallafiya: Ute Schaefer/ Halima Abbas

Edita. Halima Abbas