1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar P/M China a Berlin

May 4, 2004

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya gana da takwaransa Wen Jiabao na kasar China a fadar mulkinsa ta Berlin inda suka mayar da hankali akan dangantakar tattalin arzikin dake tsakanin kasashen biyu

https://p.dw.com/p/Bvk0
Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa P/M China Wen Jiabao
Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa P/M China Wen JiabaoHoto: AP

Wasu ‚yan daruruwan masu zanga-zanga daga kungiyoyi masu zaman kansu sun yi cincirindo a kofar fadar shugaban gwamnati Gerhard Schröder domin bayyana adawarsu da keta hakkin dan-Adam da ake yi a kasar China. Ulrich Delius, kwararren masani akan al’amuran Asiya a kungiyar kare makomar kabilun dake fuskantar barazanar gushewa a sassa dabam-dabam na duniya, ya ce kimanin mutane dubu goma ake yanke musu hukuncin kisa a kasar china a kowace shekara. Kuma sun dauki wannan mataki na zanga-zanga ne domin tunasar da shugaban gwamnati Gerhard Schröder akan wannan ta’asa. Muddin kasar ta China na fatan kyautata huldodinta da Jamus to kuwa wajibi ne ta rika girmama hakkin dan-Adam, in ji shi. To sai dai kuma a lokacin taron manema labaran da ya biyo bayan ganawar tasu babu wani zance da aka yi a game da hakkin dan-Adam illa kawai ikirarin ci gaba da tattaunawa akan wannan batu. Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko da P/M kasar ta China Wen Jiabao ya kawo nan jamus tare da mayar da hankali kacokam akan dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. An cimma daidaituwa akan kasaitattun shirye-shirye da dama na hadin guiwa tsakanin sassan biyu. Kazalika an rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi, abin da ya hada da kafa wata masana’antar na’ura mai kwakwalwa a Shangai da sayarwa da kasar China jiragen saman soja kirar Dornier da kuma wasu jiragen ruwa na jaura. Shi ma kamfanin Marsandi zai bi saun kamfanonin Vagswaja da BMW domin kera wasu motocinsa a kasar China. Schröder ya ce ba a nan kawai ta tsaya ba. A halin yanzu haka dangantakar ciniki tsakanin kasashen biyu ta kai Euro miliyan dubu 50 a shekara, kuma babbar manufarsu ita ce a ribanya wannan hulda zuwa ninki biyu nan da shekara ta 2010. Shugaban gwamnatin na Jamus dai ya kara da cewar:

Na tsayart da shawarar kai ziyara kasar China akalla sau daya a shekara. Kuma dukkanmu biyu mun dace akan mayar da wadannan ziyarce-ziyarce akan wata manufa ta al’ada ta yadda za a rika tuntubar juna tsakanin gwamnatocin kasashen biyu a hukumance, ko da sau daya ne a shekara, ko dai a nan Jamus ko kuma a can kasar China.

Bisa ga dukkan alamu dai har yau ba a tsayar da wata takamaimiyar shawara ba a game da shirin sayarwa da China masana’antar makamashin nukiliyar da ake ci gaba da sabani kanta. Schröder ya ce har yau ana bitar takardar roko da kamfanin Siemens ya gabatar. A lokacin da yake bayani game da haka Wen Jiabao nuni yayi da cewar:

Ina so in kara nanatawa cewar China zata yi amfani da tashar ce don samar da makamashi kawai. Amma zamu yi marhabin da duk shawarar da gwamnatin Jamus zata tsayar akan wannan batu. Wannan maganar ba zata gurbata kyakkyawan yanayin dangantakar tattalin arzikin dake akwai tsakanin Jamus da China ba.

A karshe P/M Wen Jiabao yayi alkawarin ba wa Jamus cikakken goyan baya a fafutukar da kasar ke yi na neman wakilci na dindindin a kwamitin sulhu na MDD.