1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Paparoma a Cyprus

June 7, 2010

Paparoma Benedict ya buƙaci ƙasashen duniya su yi hattara game da rincaɓewar rikicin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/NkKt
Paparoma Benedict na 16Hoto: AP

Paparoma Benedict na 16 ya kamalla ziyara kwanaki ukku a tsibirin Cyprus tare da yin kira da a shiga yin tattaunawa domin samar da zaman  lafiya a yankin gabas ta tsakiya kafin lamarin ya kai ga yin muni.

Paparoman wanda ya kamalla ziyara da taron aduo'in da ya yi a gaban wasu yan taiƙatatun jama'ar mabiya  ɗariƙar roman katolika a ƙasar da galibin al' umar suke bin  adinin krista na orthodox ya miƙa wani kundin ga wasu fadan cochin guda 12 waɗanda zasu tantance butun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, a taro na gaba da za a yi a fadar Vatican a cikin watan Oktober mai zuwa.

Kundin wanda ke da shafi 40, na yi kakausa suka ga mayan ƙasashen duniya da ƙungiyoyin wajen kasa waraware rikicin na yankin gabas ta tsakiya, fiye da shekaru gomai abinda ke zaman rashin kiyaye hakin bil adama da rashin muntuta ainahin samar da yanci ga Falasɗinu da ta kasance cikin tashin hankali sheakara da shekaru.

Fadar ta Vatican mai fatan ganin an kafa yantaciyar ƙasar Falasɗinu a kusa da Ira'ila ,na bayyana damuwarta dangane da yadda al' umar krista mazauna yankin ke ci gaba da yin hijira sakamakon haramcin da suke fuskanta na rashin kai ziyara a wuraran ibada na krista. A sakamakon shingayen da ƙasar Isra'ilan ta daddasa a yankunan larabawan da ta mamaye.

Papst im Nahen Osten
Pope Benedict shugaban ɗarikar Katolika na duniyaHoto: AP

Paparoman dai ya gargaɗi ƙasashen duniya da su yi hattara da kiyaye ƙara rincaɓewar rikicin na yankin gabas ta tsakiya da ka iya zama wani sabon yunƙurin zubar da jini mafi muni da kan iya faruwa.

Sanan daga bisani shugaban ɗariƙar Roman katolikan ya bayyana takaicinsa akan halin rabuwa gida biyu da ƙasar ta Cyprus take fama da shi.

A nawa bangaren ina tsamani kuma ina adu'a tare da kyakkyawan niyya na gani an samar da zaman lafiya a tsibirin Cyprus tare kuma da fatan an gagauta samar da kyakkyawar rayuwa ga al umar tsibirin.

A halin da ake ciki dai manzo musamun na majalisar dinkin duniya a ƙasar Cyprus da ke ziyara a Helsinki ,Alexandre Downerb ya baiyyana cewa majalisar Ɗinkin Duniya za ta fara zaman shawarawari domin tattauna rikicin ƙasar Cyprus da aka ƙwashe tsawon shekaru 35 ana faman yi a ƙarshen wannan shekara.

ƙasar ta Cyprus ɗin dai ta kasance a rabe gida biyu tun a shekarar 1974 bayan da ƙasar Turkiya ta mamaye arewacin tsibirin a wani juyin mulkin da yan ƙasar ta Cyprus yan kishin ƙasa masu goyon bayan ƙasar ta Cyprus ta kasance a ƙarƙashin mulkin Girka suka yi.

Mawallafi : Abdulrahman Hassan

Edita : Abdullahi Tanko Bala