1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Rice da Rumsfeld a Bagadaza

Zainab A MohammadApril 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6p

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice da na tsaro Donalds Rumsfeld sun sauka a birnin Bagadaza yau,a wata ziyarar bazata,domin tattaunawar hadin gwiwa da sabbin shugabannin Iraki,adangane da gaggauta nada gwamnatin hadaka a kasar.

Wannan ziyarar bazata na manyan jamian Amurkan biyu ,yazo ne saoi kalilan bayan sakon shugaban kungiyar Alqaeda na Iraki,Abu Musab al-Zarkawi ya bayyana ta yanar gizo gizo a kaset din Videonsa na farko ,inda yake nanata adawarsa da Washinton.A taron manema labaru da yayi da saukarsa a bagadaza sakataren tsaro na amurka Rumsfeld ya bayyana goyon bayansu wa yunkurin zababben premier ,Jawad al-maliki wajen kafa gwamnatin hadin kann alumomin irakin.

Watanni hudu bayan zaben yan majalisar dokoki a Irakin dai,shugabaninta sun kasa kafa gwamnatin hadaka,tun bayan kifar da gwamnatin sadam hussein,sakamakon sabanin raayi adangane da mukaman ministoci ,da kuma rashin cimma daidaituwa akan wanda zai jagoranci majalisar mulkin irakin.