1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR RUMSFELD A IRAQI:

May 14, 2004
https://p.dw.com/p/Bvjb
Hoto: AP

Sakamakon irin cece kucen dake ci gaba da wanzuwa dangane da abin da ya faru kann wasu yan kasar Iraqi a gidan yarin Abu Ghraib, A jiya alhamis ne ministan tsaro na Amurka ya kai wata ziyara ta musanman izuwa kasar ta iraqi.

A lokacin wan nan ziyara tashi rahotanni sun shaidar da cewa Rumsfeld ya ziyarci gidan yarin na Abu Ghraib don ganewa idon sa yadda abubuwa ke gudana a cikin sa.

Mr Rumsfeld ya shaidawa yan jaridu a lokacin wan nan ziyara cewa abin da batagarin sojin na Amurka sukayi a gidan yarin na Abu Ghrain abune daya saba da halayya irin ta Amurkawa na martaba dan adam da kuma girmamashi.

Jim kadan dai kafin barin ministan tsaron na Amurka daga iraqi izuwa gida sai daya jaddada aniyar mahukuntan na Amurka da cewa duk wadan da suka aikata wan nan mummunan aiki na take hakkokin wasu za,a tuhumesu tare da yanke musu hukuncin daya dace.

Kafin dai ziyarar ta Rusfeld Rahotnni daga kasar sun shaidar da cewa sai da dakarun sojin na Amurka suka sako wasu fursunonin kasar da dama da suke tsare dasu a cikin gidan yarin. A hannu daya kuma tare da yin alkawarin sako wasu 300 daga gidan yarin na Abu Ghraib.

Daukar wan nan mataki daga bangaren dakarun sojin na Amurka na a matsayin wata kafa ne na rage yawan fursunonin dake gidan mazan don saukakawa ragowar dake cikin sa samun yin sukuni mai ma,ana.

A wata sabuwa kuma hukumar leken asiri ta Amurka wato CIA tace babu shakka Abu Musab Al Zarqawi na hannun daman Usama Bin Laden shine ya yankewa ba a murken nan Kai a yan kwanakin baya da suka gabata.

Hukumar dai ta CIA ta tabbatar da hakan ne byan wasu kwararan bincike data gudanar kann hotun bidoyon da aka nuna a lokacin da ake gudanar da wan nan mummunan aiki.

Har ila yau a daya wajen kuma daya daga cikin shugabannin kungiyyar Alqéeda dake da zama a saudi arabia ya tabbatar da cewa kungiyar Alqeeda ce take taimakawa tsagerun kasar iraqi ci gaba da yakar sojojin taron dangi da suka mamaye musu kasa.

Babban jamian kungiyyar ta Alqeeda ya dai fadi hakan ne yau juma,a tare da karin cewa kungiyyar tasu ce tayi ajalin mutanen nan yan kasashen yamma a can kasar ta Saudi Makon daya gabata.

A waje daya kuma rahotanni daga garin Najaf sun shaidar da cewa anyi wata arangama a tsakanin dakarun sojin na Amurka da kuma magoya bayan Moqtadar sadr,wanda a lokacin akayi ta musayar wuta mai tsananin gaske.

Bugu da kari bayan sun kuma tabbatar da wata sabuwar arangama da akayi a tsakanin wadan nan bangarori biyu a can garin Karbala,wanda a lokacin da dama daga cikin mutanen bangarorin biy