1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ziyarar sabon firimiyan Japan zuwa Sin

October 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bugz

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya isa kasar Sin a yau,domin tattaunawa musamman akan batun nukiliya na Koriya ta arewa,bayan harbe harbe da akayi a bakin iyakokin kasar sun kara tada hankulan jamaa a yankin.

Shinzo abe zai tattauna da shugaba Hu Jintao da kuma Firamiya Wen Jiabao,kafin ya wuce zuwa Koriya ta arewa a gobe litinin.

A jiya asabar ne dai sojojin Koriya ta kudu suka harbin gargadi ga dakarun Koriya ta arewa da suka ratsa bakin iyakarsu.

Wannan dai shine karo na farko tun watan mayu da dakarun Koriya ta arewa suka keta shingen sojin zuwa yankin daya rabe kasashen biyu.

Abe shine shugaban Japan na farko da zai ziyarci Koriya ta arewa tun 2001.