1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Schröder Ga Afghanistan

October 11, 2004

A yau litinin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya kai ziyara fadar mulki ta Kabul, inda suka gana da shugaba Hamid Karzai, kwanaki biyu bayan zaben demokradiyya na farko a kasar Afghanistan

https://p.dw.com/p/Bvfj
Schröder a Kabul
Schröder a KabulHoto: dpa

An dai yi wa shugaban gwamnati Gerhard Schröder gaisuwar marhabin ta sha-tara ta arziki lokacin da ya isa birnin Kabul domin ganawa da shugaba Hamid Karzai a fadarsa. A dai halin da ake ciki yanzun ba tabbas a game dsa ko shin Karzai ya ci nasarar zaben, kamar yadda kasashen yammaci ke fata, domin zama shugaban Afghanistan da aka nada sakamakon zabe na demokradiyya tsantsa a wannan kasa, wacce yaki yayi kaca-kaca da ita. Sai a wajejen 30 ga watan oktoba ne ake sa ran samun cikakken sakamakon zaben na ranar asabar da ta gabata. A lokacin da yake bayani game da zaben, wanda Karzai ya kwatanta tamkar wani lamari na tarihi, shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder cewa yayi:

A hakika ba kuskure ba ne da a kwatanta wannan zabe a matsayin wani lamari na tarihi, domin kuwa wannan babban ci gaba ne aka samu akan hanyar tabbatar da mulkin demokradiya da kwanciyar hankali a kasar Afghanistan kuma na sikankance cewar akwai wasu matakan da zasu biyo-baya nan gaba.

Da farkon fari dai Schröder ya fara ya da zango ne a sansanin sojan kiyaye zaman lafiya na Jamus, inda ya yaba musu akan gudummawar da suke bayarwa domin kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Afghanistan. Ziyarar ta Schröder ta fuskanci suka mai tsananin gaske inda da yawa daga masu takarar neman kujerar shugabancin kasar suka zargi shugaban gwamnatin na Jamus da nuna son kai ga Hamid Karzai. Mir Muhammad Mahfuz Nedahi ya ce wannan ziyarar wata kyakkyawar alama ce dake nuna cewar Jamus dai alla-alla take yi ta ga cewar Karzai ne ya lashe zaben. Shi ma dan takara Abdul Latif Pedram ya gabatar da kira ga kasashen Turai baki dayansu da su mayar da hankali wajen ba da goyan baya ga manufar dora kasar Afghanistan kan tsarin mulkin demokradiyya tsantsa, a maimakon nuna son kai ga wani dan takara guda daya kwal. Amma bisa ga ra’ayin Schröder wannan ziyarar babu wani aibu tattare da ita saboda Karzai shi ne shugaba mai ci a halin yanzu haka. A nasa bangaren shugaba Karzai sharhi yayi game da ziyarar yana mai cewar:

Bisa ga dukkan alamu masu korafin ba su ankara ba ne da cewar wannan ziyara ba ziyara ce ta taya murnar nasarar zabe ba. Bugu da kari kuma gwamnatin rikon kwaryar dake ci zata ci gaba da tafiyar da al’amuran mulki har ya zuwa lokacin da za a nada wata sabuwar gwamnati ta gaba. A saboda haka dukkan al’umar Afghanistan na mika godiya ga shugaban gwamnati Schröder a game da ziyarar da ya kawo wa kasar a daidai wannan lokacin da ake ciki. Al’umar Afghanistan na murna da ziyarar daidai da yadda suke doki a game da wannan zabe.