1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Schröder ga Libiya

October 14, 2004

A gobe juma'a idan Allah Ya kai mu shugaban gwamnatin Jamus Gerhard schröder zai kai ziyararsa ta farko ga kasar libiya, inda zai gana da shugaba Ghaddafi a fadar mulki ta Tripoli

https://p.dw.com/p/BvfZ

Bayan tofin Allah tsine da aka rika yi masa a matsayin dan tsagera dake rufa ayyukan ta’adda a sassa dabam-dabam na duniya a zamanin baya, a yanzu an shigar da shugaban Libiya Mu’ammar Ghaddafi a cikin jerin bayin Allah da ya kamata a rika cude-ni-in-cude-ka da su a al’amuran siyasa da tattalin arziki da manufofin tsaro da ‚yan gudun hijira. Ba zato ba tsammani shugaba Ghaddafi ya sosa wa kasashen yammaci daidai inda ke yi musu kaikayi lokacin da ya fito fili yana mai fatali da shirin Libiya na mallakar makaman kare-dangi da biyyan kudaden diyya akan hare-haren da ake zargin kasar da hannu a ciki. A baya-bayan nan ne Shugaba Ghaddafi mai shekaru 61 da haifuwa yayi alkawarin biyan diyyar dalar Amurka miliyan 35 ga mutanen da wani hari na ta’addancin da aka kai kan wani gidan rawa a birnin Berlin a shekarar 1986 ya rutsa dasu, wadanda galibi ‚yan kasar Amurka ne. Mutane uku suka yi asarar rayukansu sannan wasu metan suka ji rauni sakamakon wannan hari. Gwamnatin Jamus tayi madalla da wannan shawara ta biyan diyya da Libiya ta tsayar kuma ta haka aka share hanyar sake kama huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Wannan matakin zai taimaka a bude wani sabon babi na huldodin dangantaku, ba ma kawai tsakanin Libiya da Jamus kadai ba, kazalika har da sauran kasashen Kungiyar Tarayyar Turai. A koyi da kasar Amurka, a '‚an kwanakin da suka wuce kungiyar ta tsayar da shawarar dage dukkan takunkumin da ta kakaba wa Libiya tsawon shekaru 20 da suka wuce, abin da ya hada har da takunkumin haramta sayarwa da kasar ta arewacin Afurka makamai. A lokacin da yake bayani game da haka ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer cewa yayi:

2. O-Ton Fischer:

"Was die...

Ita dai Libiya ta fito fili ta bayyana niyyarta ta kakkabe hannuwanta daga miyagun makamai na guba da na kare-dangi, kuma a ganina wajibi ne a nakalci lamarin da idanun basira. Hakan shi ne a’ala akan manufa.

Kasar Italiya dai tafi kowa alla-alla, wajen ganin cewar an daidaita huldodin dangantaku da kasar Libiya. Libiya dai kasa ce da Allah Ya fuwace mata albarkatun mai da gas, kuma tuni aka bude kofar hada-hadar zuba jari da neman kwangila a kasar. Kawo yanzun dai Jamus ce ta biyu a baya ga kasar Italiya a tsakanin kasashen dake da kakkarfar dangantakar ciniki da Libiya, amma a yanzu sun fara fuskantar barazana daga kasar Amurka. Ta la’akari da haka wannan ziyarar ta shugaban gwamnati Gerhard Schröder take da muhimmanci matuka ainun, inda aka shirya kaddamar da bikin bude wata sabuwar rijiya da kuma balaguron wasu rijiyoyin na mai a kasar ta Libiya. Wani muhimmin abu kuma shi ne hadin kai da ake nema daga kasar Libiya domin tinkarar matsalar nan ta ‚yan gudun hijira dake bi ta tekun bahar rum domin shigowa nahiyar Turai. To sai dai kuma duk da wannan sabon babi na dangantaku da aka shiga tsakanin Libiya da kasashen yammaci, akwai wasu dake gargadin taka tsantsan, saboda a ganinsu mai yiwuwa shugaba Ghaddafi kokari yake yi ya fake da guzuma domin ya harbi karsana.