1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaba Abbas na yankin Palasdinawa a Jordan

February 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuS3

Shugaban yankin Palasdinawa Mahmoud Abbas yayi kira ga Izraela data amince da yarjejeniyar hadin kann yankin,wadda ya rattaba hannu tare da kungiyar hamas mai mulki ,akokarin da ake na samarda zaman lafiya mai dorewa a wannan yankin.A ziyarar dayake kaiwa kasashen larabawa,shugaba Abbas yace bisa ga yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka da suka cimma da kungiyar Hamas,Izraela bata da wani dalili a halin yanzu na kin amincewa komawa teburin tattaunawa da magabatan yankin palasdinawan.A nashi bangaren prime minista Ehud Olmert na Izraelan yace kada wannan yarjejeniyar,ta hana Hamas daga darajawa kiran da kasashen duniya ke mata na watsi da miyagun ayyuka,tare da laakari da Izraela a matsayin yantacciyyar kasa.Akan hakane yayi kira ga shugabannin kasashen turai da kada su matsa daga matsayinsu kann wannan batu.Dayake jawabi a kasar Jordan domin bayyanawa Sarki Abdulla yarjejeniyar hadin gwiwa da aka cimmawa,Shugaba Abbas yayi kira ga Izraela data daina tsoma baki a siyasar cikin gida na yankin Palasdinawa.