1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaba Bush a China

November 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvKJ

A hukumance a yau lahadi shugaban Amirka GWB ya fara ziyarar aikin yini 3 a China inda ya halarci wani zaman ibada a wani coci. Jami´ai sun ce Bush na son ya aike wani sako ne ga hukumomin China da su kara ba da ´yancin yin addini a cikin kasar. Daga bisani Bush ya tattauna da shugaba Hu Jintao, inda shugabannin biyu suka mayar da hankali akan rarar ciniki da China din ke samu akan Amirka. Shugaba Hu ya tabbatarwa Bush cewa gwamnatinsa zata ci-gaba da aiwatar da canje-canje don daidaita darajar takardu kudin kasar. To amma ya ce China ba zata amince da ´yancin Taiwan ba. Bush ya fara rangadin mako daya a nahiyar Asiya ne tare da yin kira ga China da ta bari kyakkyawan tsarin demukiradiya a Taiwan babbar abokiyar gabar gwamnatin Beijing ya zama mata misali wajen aiwatar da canje-canjen siyasa. A gobe litinin shugaban na Amirka zai kammala rangadin na Asiya bayan ya ziyarci Mongolia.