1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Shugaba Kagame Na Ruwanda a Berlin

July 1, 2004

A ziyarar da yake ga Jamus shugaba Kagame na kasar Ruwanda ya gana da ministan harkokin waje Joschka Fischer da ministar taimakon raya kasashe masu tasowa Heidemarie Wieczorek-Zeul

https://p.dw.com/p/BviV
Kagame da Kabila lokacin ganawarsu a Abujan Nijeriya
Kagame da Kabila lokacin ganawarsu a Abujan NijeriyaHoto: AP

A hukumance dai an cimma zaman lafiya tsakanin Ruwanda da makobciyarta janhuriyar demokradiyyar Kongo tun a shekara ta 2002. Bayan yaki na tsawon shekaru biyar dukkan kasashen biyu sun rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya a Pretoria, fadar mulkin Afurka ta Kudu (ATK). Amma wannan sabon hali na zaman dardar da aka shiga ya samu ne sakamakon farmakin da ‚yan tawaye suka kai a garin Bukavu dake kan iyakar gabacin kasar Kongo. Shugaban kasar kongo Joseph Kabila na yana zargin Ruwanda da rugfa wa ‚yan tawayen baya kuma a saboda haka ya tura sojoji dubu 20 zuwa iyakokin kasashen biyu. Nijeriya ta tsoma baki inda ta kira taron gaggawa tsakanin Kabila da Kagame domin lafar da kurar rikicin. A lokacin da tashar DW take hira da shi, shugaba Kagame dake balaguron Jamus yanzu haka cewa yayi:

Matsalar dake akwai ita ce. Mun janye sojojin Ruwanda daga kasar kongo, amma a daya bangaren ba a shawo kan rikicin dakarun sa kai na Hutu da tsaffin sojojin dake kasar Kongo ba. Wannan shi ne ainifin abin dake gurbata yanayin dangantakarmu da kasar ta Kongo. Wannan shi ne abin da muka dukufa a kai yanzu haka. Daga bisanin nan na sadu da shugaban kasar Kongo Kabila a Abujan Nijeriya a karkashin jagorancin shugaba Obasanjo. Mun sake bitar rikicin sannan dukkanmu muka hakikance cewar wajibi ne yarjejeniyar Pretoria ta zama ginshikin dangantakarmu.

Bayan kisan kiyashin da ya wanzu a Ruwanda a 1994 da yawa daga ‚yan hutu dake da alhakin ta’asar sun tsere zuwa kasar Kongo, a cewar Kagame, wanda ke shugabancin kasar Ruwandar tun daga shekara ta 2000. A karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar ta Pretoria gwamnatin kasar Kongo tayi alkawarin kwance damarar makaman dakarun Hutun, amma bisa ga ra’ayin Kagame, bata cika wannan alkawari ba. Ya ce yarjejeniyar ta zaman lafiya kome ingancinta ba zata amfanar da kowa ba, sai fa idan an aiwatar da ita. Ya dai bayyana fatan cewar Kungiyar Tarayyar Afurka da MDD zasu taimaka wajen lafar da kurar wannan rikici. A nata bangaren gwamnati a fadar mulki ta Berlin tayi kira ga shugaba Kagame da yayi bakin kokarinsa wajen lafar da kurar rikicin sannan tayi alkawarin ba shi goyan baya bisa manufa. Kasar Ruwanda dai tana fama da matsaloli na tattalin arziki da bunkasar yawan jama’a ta yadda ta dogara kacokam akan taimako daga ketare wajen cike gibin kashi 40% na kasafin kudinta. A saboda haka babban abin da ta sa gaba shi ne magance matsalar ta tattalin arziki da kuma dinke barakar da ta samu tsakanin al’umarta sakamakon kisan kiyashin da ya wanzu a shekarar 1994, in ji shugaba Kagame.