1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Shugaba Mahmud Abbas na yankin Palasdinu a Asia

Zainab A MohammadMay 20, 2005

Palasdinu ta nemi goyon bayan kasashen Pakistan,da Japan,da Sin da India wajen samun yantacciyar kasa

https://p.dw.com/p/Bvbn
Hoto: AP

Shugaban Palasdinawa Mahmud abbas ya bayyana cewa bashi da niyyan dage zaben yan majalisar dokoki da aka tsara gudanarwa ranar 17 ga watan Yuli a yankinsa.

Shugaban na Palasdinawa yayi wannan furucin ne a yayinda yake hira da manema labarai a birnin New delhin kasar India acigaba da ziyara dayakeyi a nahiyar Asia.

A jiya nedai Mahmud Abbas ya isa kasar ta India domin ziyara yini biyu,wanda akesaran zai karfafa goyon bayan India wa kokarinda palasdinu takeyi na cimma yantacciyar kasa.

Wannan dai itace ziyarar shugaba Abbas a yankin Asia ta farko tun daya haye karagar mulki bayan marigayi yasser Arafat a watan Janairu.

A ziyarar sa a Pakistan dai,shugaban na Palasdinawa ya bayyana cewa shugaba Pervez Musharraf nada muhimmiyar rawa dazai taka ac yunkurin samarda zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Bugu da kari a ziyararsa a kasar Japan ya samu nasaran alkawarin dala million 100 na tallafi daga gwamnatin kasar,domin tallafawa zirin gaza sakamakon janyewa Izraela,inda yayi gargadin cewa duk da nasarori da ake samu,har yanzu da sauran rina a kaba wajen warware rikicin yankin.

Tun a jiya nedai shugaban Palasdinawan ya gana da Prime minister Manmohan Singh da minstan harkokin waje Natwar Singh da kuma shugabar jammiyar mulkin kasar Sonia Gandhi,inda nan ma ya samu cikakken goyon bayan magabatan India wajen samarwa Palasdinawa yantacciyar kasarsu.

Gwamnatin hadin kan kasa da aka nada a India a bara dai,ta dauki salon a musamman wajen warware rikicin yankin gabas ta tsakiya,sabanin rusasshiyar gwanatin hindu data gabata.

A matsayinta na shugabar kungiyar kasashen yan baruwammu ,India tayi watsi da Izraela a baya,amma a shekara ta 1992,New Delhi a karkashin gwamnatin hadin kai a wancan lokaci ta kaddamar da dangantakar diplomasiyya da wannan kasar yahudawa,da zummar samar da zaman lafiya a yankin.Dangantaka na kut da kut ya dada ingantuwa tsakanin India da Izraela tun bayan kafa gwamnati a karkashin jagorancin jammiyar yan Hindu a shekara ta 1998,inda bangarorin biyu suka rattaba hannu a yarjeniyoyin tsaro na biliyoyin dala,tare da hadin gwiwa wajen yaki da ayyukan yan taadda.A yanzu haka Izraela itace kasa ta biyu dake sayarwa India makamai.

Ana dai ganin cewa wannan ziyara ta shugaba Mahmud Abbas zai taimaka matuka gaya wajen daidaita dangantakar India da Izraela da kuma Palasdinu.

Daga kasar Japan dai shugaban palasdinawan ya yada zango a birnin Beijin din kasar Sin inda ya jaddada cewa zaayi maraba da masu tsattsauran raayi na yankin watau Hamas cikin zaben yan majalisar dokoki da zai gudana watan Yuli,kuma nan gaba zaa bawa wannan kungiya dammar shiga harkokin gwamnati.

A birnin Tokyo kuwa ya fadawa kafofin yada labaru cewa, sanya kungiyar hamas cikin harkokin gudanar da mulki a yankin zai taimaka matuka gaya wajen warware rikice rikice da ake samu ba sai anyi amfani da karfin soji ba.

A mako mai zuwa nedai ake saran shugaban na palasdinawa zai ziyarci fadar gwamnati ta white house a Amurka,domin ganawa da shugaba George W Bush,a kokakarin warware rikicin yankin gabas ta tsakiya da tabbatarwa Palasdinawa yantacciyar kasarsu nan gaba.