1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Washington

October 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvOe

Shugaban hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa Mahmud Abbas ya isa birnin Washington inda zai gana da shugabn Amirka GWB. Tattaunawar da zasu yi a fadar White House ita ce ta farko tun bayan janyewar Isra´ila daga Zirin Gaza a cikin watan jiya. Jami´an Falasdinawa sun ce Abbas zai bukaci Bush da ya matsawa Isra´ila lamba ta rushe matsugunan Yahudawa da aka gina ba bisa ka´ida ba tare da yin kira ga Isra´ila da ta dage sabuwar dokar da ta kafa ta hana Falasdinawa amfani da manyan hanyoyin mota a Gabar Yamma da Kogin Jordan. A nasa bangaren ana sa ran Bush zai yi kira ga Abbas da ya kara daukar sahihan matakan hana hare-haren ´yan takifen Falasdinawa akan Isra´ila, musamman bayan wani harin da aka kai kan Yahudawa ´yan share wuri zauna a ranar lahadi da ta gabata.