1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR SHUGABAN FARANSA A LIBYA.

Zainab Mohammed.November 24, 2004
https://p.dw.com/p/BveR
Shugaba Jacques Chirac na Faransa.
Shugaba Jacques Chirac na Faransa.Hoto: AP

A yau ne Shugaba Jacques Chirac na kasar Faransa ke fara wata ziyarar aiki a Libya,ziyarar dake zama na farkon irinsa a bangaren shugaban faransan,wanda kuma ke dada tabbatar da komowan shugaba Mammar Ghadafi na Libya cikin harkokin dangantaka da kasashen duniya.

A bangaren kasar ta faransa,wannan ziyara na mai zama wata dama ce ta shiga harkokin kwangila da ciniki na kut da kut ,wanda zai b iyo alkawarin da shugaba Ghadafi yayi na kawar da shingen tattalin arziki daya dabaibaye,wannan kasa mai dunbin albarkatun man petur.

A can birnin Tripoli,fadar kasar ta Libya an jera tutocin Faransa akan tituna,wanda ke nuna alamun marabtan shugaba Chirac ,wanda ministocinsa uku ke rufa masa baya,da ayarin kwararrun yan kasuwa.

Tattaunawarsu da Ghadafi dai,a wannan ziyara tasa zai kunshi batutuwa da dama da suka hadar da rikicin Iraki,da Nahiyar Afrika da ,da harkokin taaddancin baya ga dangantaka ta inganta tattalin arziki.

Wannan ziyara ta shugaban Faransa dai ya biyo bayan ganawa da Shugaba Ghadafi yayi ne da wasu shugabanin turai ,ciki harda Tony Blair na Britania,Gehard Schroder na Jamus,da prime ministan Italia Silvio Berlusconi,wadanda baki dayansu suka bukaci Libya data duka wajen farfado da tattalin arzikita.

Shugaba Ghadafi wanda ya haye karagar mulki ta hanyar juyin a shekarata 1969,ya amince da yarjejeniyoyi da dama na diplomasiyya tun a shekara data gabata,bayan amincewarsa da dakatar da kera makamai masu guda,da haramta ayyukan taaddanci ,tare da amincewa da daukan alhakin harin bomb din nan na jiragen Lockerbie da UTA,a shekarun 1980s.

A dangane da hakane kasar Amurka da kasashen turai suka dage wasu takunkumi da aka kakabawa Libyan ,bayan wadannan hare haraen biyu.A wanatan daya gabata ne Belgium ta dage takunkumin na makamai akan Libyan.

Tun dai a watan Janairun wannan shekara ne dangantaka ta sake farfadowa tsakanin Libya da Faransa,bayan cibiyar da Dan Ghadafoi,Saif al-Islam ke jagonta ,ya amince da biyan diyyan tsabar kudi dala million 170,wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin bomb da aka afkawajirgin UTA din a sararin samaniyan Arewacin Afrika,inda mutane 170 suka salwanta.Tun bayan nan ne ministan harkokin ciniki Francois Loos da na harkokin wajen faransan Michel Barnier,suka kai ziyara birnin Tripoli,ayayinda shima premiern Libya Shukri Ghanem ya ziyarci Paris.

Wadanda ke marawa Shugaban Faransan baya a wannan rangadin aiki a Libya dai,sun hadar da ministocin Ciniki,da harkokin kasashen waje,da na sufuri Gilles de Robien.

A hiran da akayi dashi gabannin wannan ziyara,shugaba Ghadafi ya jaddada muhimman hadin kann Libya da Faransa wajen cigaban Afrika.Shugaba Chirac zasi kwana a Tripoli yau,kana gobe ya zarce zuwa Birnin Ouagadougou,a kasar Burkina faso ,domin halartan taron kasashe masu magana da harshen faransanci.

Faransawan dai na zawarcin samun kwangiloli a masanaantun man Libyan,da harkokin sufurin sama ,banki,bangaren wutan lantarki ,muhalli da kuma harkokin yawon shakatawa.