1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban gwamnatin Jamus a Turkiyya

Zainab A MohammadMay 4, 2005

Shugaba Gehard Schroder na Jamus ya gana da Recep Erdogan na Turkiyya

https://p.dw.com/p/Bvc9
Hoto: dpa

Shugaban gwamnatin Jamus Gehjard Schroder,yayi kira ga kasar Turkiyya data aiwatar da dukkan gyare gyaren da ta cimma kuduri akansu ta fannin democradiyya.

Shugaba Gehard Schroder yayi wannan kiran a cigaba da ziyarar yini biyu daya fara jiya a wannan kasa dake da musulmi,a matsayin masu rinjaye daga alummominta,kana kuma bukaci Turkiyyan datayi kokarin cimma bukatun kungiyar gammayyar Turai Eu ,tare da ki data bawa alummomin kristocin kasar yanci,wadanda sune zasu bawa kasar daman amincewa da ita a kungiyar ta EU.

Schroder wanda ke zama daya daga cikin magoya bayan Turkiyyan wajen hadewa da kungiyar turan,ya bada tabbacin cewa wakilan zasu bude kofar fara tattaunawa da Ankara batun amincewa da ita kamar yadda aka tsara ranar 3 ga watan oktober idan mai duka ya kaimu.

Bayan ganawarsa da prime minister Recep Tayyip Erdogan,shugaban gwamnatin na jamus ya fadawa yan jarida cewa kamata yayi a aiwatar da dukkan kuduri da aka cimma da kuma wadanda ke kunshe cikin kundun tsarin mulkin wannan kasa.Dayake amsa tambayr manema labarai dangane da matsayin faransa kan kundun tsarin mulkin kungiyar ta Eu,wanda ´zaayi kuriar raba gardama ranar 29 ga wannan wata,Schroder ya tabbatar dacewa babu wata kuriar raba gardama a koina a nahiyar turai dazai,kawo cikas a shirin fara tattauna batun shigan turkiyya kungiyar.

Ya jaddada bukatar turkiyya data darawa bukatun kungiyar Eu na bawa wadanda ba musulmi yancin gudanar da harkokinsu ba tare da matsin lamba ba,musamman Christoci da yahudawa dake wannan kasa,inda ya kara dacewa yancin addini a koina na mai zama tanbarin turai,kuma kamata yayi Turkiyya tabi sawu wajen bawa kowa yancin yin addininsa.

Yanzu haka dai Turkiyya na fuskantar matsin lamba dangane da wasu dokokin ta na hana wadanda ba musulmi ba,gudanar da harkokinsu na bauta,tare da bukatar bude cibiyar nazarin addinin Krista na Girka da aka rufe sama da shekaru 30 da suka gabata a birnin Istambul.

Bugu da kari shugaba Gehard Schroder yayi amana da yunkurin Turkiyya na kafa hukumar hadin gwiwa da Armenia,wajen binciken zargin da akayiwa Turkawan Daular Ottoman ,kan cewa sunyiwa Armeniawa kisan gilla lokacin yakin duniya na daya.Yace burinsu ne suga cewa dangantaka ya ingantu tsakanin Turkiyya da Armenia,domin Jamus a shirye take ta tallafa ta wannan bangaren.

Lokacin yakin duniya ta daya dai,Jamus da daular Ottoman ,inda daga nan ne aka samu janhuriyar turkawa na yanzu ,na masu kasancewa aminan juna,a wannan lokaci ne kuma akayi kisan kiyashi wa Armaniyawan.

Yanzu haka dai Turkiyya na fuskantar matsin lamba da yan siyasar turai ciki harda jammiyyun adawan jamus,na binciken wannan kisan daya gudana tsakanin 1915-17,tare da biyyan diyya,idan har Ankara na bukatar amincewa a kungiyar EU.

Shugabannin biyu kazalika sun tattauna batun rikicin tsibirin Cyprus,wanda shima ke kasancewa Turkiyyan kadangaren bakin tulu wajen hadewa da kungiyar ta EU,inda shugaban gwamnatin Jamus yayi alkawarin bada agajin euro million 259,a madadin kungiyar eu,domin tallafawa bangaren wannan tsibiri dake karkashin Turkiyya.A bara nedai kungiyar Eu tayi alkawarin bada wannan agajin a matsayin tukuici wa turkiyya,saboda goyon bayan da cyprot na wannan kasa ya bawa shirin zaman lafiya na mdd,wanda kuma a daya hannu yasha suka daga tsibirin Cyprot dake bangaren Girka,wadda ta samu hadewa da EU,a watan mayun bara.

Jamus dai na mai kasancewa babbar aminiyar cinikayyan Turkiyya,kana akwai turkawa kimanin million biyu da dubu dari biyar dake zauna cikin jamus.Bugu da kari Schroder zai gana da shugaba Ahmet NecdetSezer,kafin ya wuce zuwa birnin Istambul,inda zai gana day an kasuwan Jamus da Turkiyya dake zaune a wannan birni.