1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Shugaban Iraki Ga Jamus

September 8, 2004

A yau laraba ne shugaban kasar Iraki Ghazi el Jawar yake fara ziyararsa ta yini biyu ga fadar mulki ta Berlin, inda zai mayar da hankali ga matsaloli na kudi da kuma gudummawar da jamus zata iya bayarwa a fafutukar neman zaman lafiyar Iraki

https://p.dw.com/p/Bvgf
Shugaban kasar Iraki yana ganawa da jakadan Jamus a Bagadaza
Shugaban kasar Iraki yana ganawa da jakadan Jamus a BagadazaHoto: AP

Muhimmin abin dake tattare a zuciyar shugaban kasar Iraki Scheikh Ghazi El Jawar a ziyararsa da yini biyu ga Jamus shi ne maganar kudi da neman goyan bayan siyasa. Zai yi bakin kokarinsa wajen ba wa Jamus kwarin guiwar kara shiga a dama da ita a fafutukar neman zaman lafiyar Iraki. A wannan bangaren kuwa babu wani sabani tsakaninsa da ministansa na harkokin waje Hoshjar Sebri, wanda a cikin hirar da wata tashar rediyon Jamus tayi da shi ya danganta zama ‘yar rakiya da Jamus tayi a game da al’amuran sake gina Irakin da kyamar da kasar ta nunar tun da farkon fari da yakin Irakin. Sebri yayi batu a game da wani sabon yanayin da aka shiga a kasar Iraki, wanda a fakaice ke ma’anar gwamnatin wucin gadi mai ikon cin gashin kanta da aka nada a fadar mulki ta Bagadaza a karshen watan yunin da ya wuce. Ko da yake, kamar yadda su kansu ‘yan kasar iraki suka hakikance, ita gwamnatin ‘yar jeki na yi ki ne dake rawa da bazon Amurka, amma an samu wani dan canji idan an kwatanta da zamanin baya. Babban misali shi ne sassaucin da ake wa kamfanoni daga kasashen da suka ki tsoma hannu a yakin Irakin domin zuba jari a kasar a cikin makonnin baya-bayan nan. To sai dai kuma manufofi na dogon turanci da tabarbarewar tsaro na ci gaba da hana ruwa gudu bisa manufa. Wannan mawuyacin hali da ake ciki yana daya daga cikin dalilan da suka sanya kamfanonin Jamus ke daridari da maganar zuba jari a Iraki. Kawo yanzun dai kamfanonin na Jamus dake da jari a Iraki yawansu bai zarce kamfanoni 60 ba, kamar yadda aka ji daga bakin Reinhard Avemman, wakilin ‘yan kasuwar Jamus a game da al’amuran Iraki, wanda kuma yake da ofishinsa a Amma fadar mulkin kasar Jordan. Bugu da kari kuma har yau gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta ki ta tallafa wa kamfanonin da asusun nan na Hermes, wanda akan yi amfani da kudadensa domin cike gibin kamfanonin Jamus a ketare. Daya matsalar kuma ita ce dimbim bashin da Irak ta ciwo daga Jamus a karkashin mulkin tsofon shugaba Saddam Hussein. Gwamnati a Berlin na daridari wajen yi wa Irakin sassaucin basussukan saboda dimbim arzikin mai da Allah Ya fuwace mata. An dai saurara daga ministan harkokin waje Joschka Fischer jim kadan kafin ziyararsa ga Yankin Gabas Ta Tsakiya cewar Jamus zata ba da gudummawa gwargwadon ikonta domin cimma zaman lafiyar Iraki a karkashin kudurin kwamitin sulhu na MDD ko da yake kasar ba zata ba da wata gudummawa ta sojojinta ba. A halin da ake ciki yanzun tuni aka kulla dangantakar al’adu tsakanin kasashen biyu. An fara ba da skolaship ga dalibai daga Iraki domin neman karin ilimi a jami’o’in Jamus hade kuma da taimakon litattafai masu yawa ga sashen koyar da adabin Jamusanci a jami’ar Bagadaza.