1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban Sin zuwa Afrika

April 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0n

Shugaban kasar Sin,Hu Jintao,ya fara ziyararsa zuwa wasu kasashen nahiyar Afrika,inda a yau yake isa kasar Morocco,inda zai tattauna akan harkokin ciniki,tattalin arziki,kimiya da fasaha,tare hadin kan aladu da kula da lafiya.

Wannan ziyara ta Hu wanda ya faro daga Amurka zuwa Saudiya,zata kai shi kuma zuwa kasashen Nigeria da Kenya.

A 2002 ne sarki Muhammad na 6 ya kai ziyara zuwa kasar ta Sin,a zamanin shugabancin Jiang Zemin.

Kafin barinsa kasar saudiya a jiya lahadi,shugaba Hu,ya baiyana aniyar kasar sin na aiki tare kafada da kafad da kasar ta Saudiya,dama wasu kasashen larabawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.