1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugabar gwmnatin Jamus a Biritaniya

November 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvJd

Aci gaba da ziyarar aiki da take , a yanzu haka shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na kasar Biritaniya don saduwa da takwaran ta wato,Tony Blair.

Babbar ajanda da shugabannin biyu zasu fi mayar da hankali kai a lokacin ganawar tasu zata shafi batun sabani ne da aka samu a kasafin kudi na kungiyyar tarayyar Turai, wato Eu.

Kafin dai isar tata kasar ta Biritaniya a jiya ,Angela Merkel ta kai irin wannan ziyara izuwa kasar Faransa a inda ta sadu da shugaba Jack Chirac.