1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Steinmeier a Afghanistan

August 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bum5

Ministan harkokin wajwen Jamus Frank Walter Steinmeir ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a ƙasar Afghanistan. Steinmeir zai gana da shugaba Hamid Karzai da sauran ƙusoshin gwamnati. Manyan batutuwan da ake sa ran za su tattauna a kai sun haɗa da yawaitar tarzoma a Afghanistan da kuma kokarin da ake wajen sake gina ƙasar. Ziyarar ta Steinmeir ta zo a daidai lokacin da aka yi ƙazamin ɗauki ba daɗi tsakanin Yan tawayen Taliban da sojojin NATO dana Afghanistan a kudancin kasar. A kalla yan tawayen Taliban ɗin 70 ne suka rasa rayukan su da kuma sojin Afghanistan su biyar waɗanda suka gamu da ajalin su yayin wata arangama a lardin Kandahar. A ranar Talata, Ministan harkokin wajen na Jamus zai kai ziyara ga dakarun Jamus na Bundeswehr a garuruwan Mizaril Sharif da kuma Kunduz. Watanni biyu da suka gabata, Jamus ta karɓi ragamar gudanarwa na dakarun sojin NATO ƙarƙashin jagorancin sojojin kiyaye zaman lafiya na ISAF a kudancin Afghanistan.