1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Steinmeier a yankunan Falasdinawa

February 14, 2006

A karon na farko tun kama aikinsa, ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya kai ziyara a birnin Ramallah, inda ya gana da takwaran aikinsa na Hukumar Falasdinawa, Nasser al-Kidwa da kuma shugaban Falasdinawan mai barin gado Mahmud Abbas.

https://p.dw.com/p/Bu1j
Steinmeier (dama) tare da takawran aikinsa na Hukumar Falasdinawa, Nasser al-Kidwa.
Steinmeier (dama) tare da takawran aikinsa na Hukumar Falasdinawa, Nasser al-Kidwa.Hoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Wannan ziyarar dai, ita ce ta farko da ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya kai a yankunan Falasdinawa tun kama aikinsa. Yayin da ya gana da takwaran aikinsa na Hukumar Falasdinawan Nasser al-Kidwa, ministan ya sake nanata abin da tun da farko ya fada bayan shawarwarin da ya yi da ministan harkokin wajen Isra’ila, Tsippi Livni, a birnin kudus ne, inda ya ce Turai dai ba za ta yi hulda da kungiyar Hamas ba sai ta cika wasu ka’idoji. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai game da wannan batun, Steinmeier ya bayyana cewa:-

„Na dai yi kokarin bayyana matsayin da Turai ta dauka ne na cewa, ba za mu iya aiki da wata Hukuma a yankunan Falasdinawa ba, mu ci gaba da tuntubar juna, da ba da taimakon da muka saba bayarwa ba, sai wannan Hukumar ta kakkabe hannunta daga duk wasu tashe-tashen hankulla, ta amince da wanzuwar Isra’ila tamkar kasa, sa’annan kuma ta rungumi duk wasu yarjejeniyoyin da aka cim ma kawo yanzu, tsakanin Hukumar Falasdinawan da Isra’ila.“

A nasa bangaren, ministan harkokin waje na Hukumar Falasdinawan, al-Kidwa, ya yi kira ga kungiyar Hadin Kan Turai da ta ci gaba da ba da taimakon kudade ga Hukumar, duk da sabuwar gwanatin da za a samu ta masu bin ra’ayin islama. A nasa ganin dai, shirye-shiryen da sabuwar gwamnatin za ta gabatar ne ke da muhimmanci, amma ba jami’an da za su shugabance ta ba. Wato a nan dai, yana kira ne ga takwaran aikinsa na Jamus, Steinmeier, da ya dubi bambancin da akwai tsakanin kungiyar Hamas din da gwamnatin hadin kan duk Falasdinawa da za a kafa, wadda za ta kunshi duk jam’iyyun da ke da wakilci a majalisar.

Shi dai Steinmeier, ya kuma gana da shugaban Falasdinawa mai barin gado, Mahmoud Abbas, a birnin na Ramallah. A daidai lokacin da suke shawarwarin ne kuma, jaridar nan ta New York Times ta buga wani rahoto mai ta da hankali, inda ta ce gwamnatin Amirka da Isra’ila sun tsara wa shirin sirri na dagula wa sabuwar gwamnatin Falasdinawa karkashin kungiyar Hamas al’amuranta, tun ma kafin a kafa ta. Jaridar ta ce ta samo wannan labarin ne daga wasu majoyoyi masu tushe, wadanda suka kunshi jami’an Isra’ilan da kuma jami’an diplomasiyya na kasashen Yamma. daya daga cikin matakan dagula wa Hamas din al’amuranta ne kuma, janyo yunwa a yankunan Falasdinawan. Amirka da Isra’ila dai, inji jaridar, sun tanadi soke duk taimakon kudi da suke bai wa Hukumar, su kuma yunkuri shawo kan gamayyar kasa da kasa su yi mata saniyar ware. Ta hakan dai, Hukmar z ata kasance cikin wani matsin lamba ne, har ya kai ga rushewar gwamnatin da ta kafa, abin da zai janyo gudanad da sabon zabe, inda Isra’ilan da Amirka ke fatar cewa, abokiyar Huldarsu, wato kungiyar Fatah, za ta sake hawa karagar mulki.