1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Tony Blair a Jamus

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 17, 2006

Angela Merkel da Tony Blair,sun tattauna game da batutuwa da dama da suka shafi ci gaban atariyar turai da kuma hulda da wasu kasashe,a wajen nahiyar.

https://p.dw.com/p/Bu1c
Hoto: AP

Bayan tattaunawar tasu akan batutuwan tattalin arzikin kasashen turai,batun gabas ta tsakiya da kuma shirin nukiliya na Iraqi cikin wasu batutuwa,shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel da Firaministan Burtaniya Tony Blair,sun sake jaddada cewa,dole ne kungiyar Hamas ta dakatar da kai hare hare tare da amincewa da kasar Israila a matsayin kasa mai yancin kanta,muddin dai tana son kasashen duniya su taimaka mata.

Blair yace,kasashen duniya suna mutunta nasara da Hamas ta samu a zaben yankin Palasdinawa,amma a cewarsa,Hamas tana bukatar taimakon kasashen duniya idan tana neman ci gaba,wannan kuwa inji shi,itace hanya mafi aala.

A game da batun Iran,shugabannin biyu, sun baiyana fatar cewa,zaa magance matasalar nukiliya na Iran ta hanyar diplomasiya.

Kasahen Burtaniya jamus da Faransa dai sun gudanar da taruka da dama cikin watanni uku a kokarinsu na tabbatar da cewa shirin nukiliya na Iran na zaman lafiya ne.

Blair kuma ya maida martani game da kira da Iran tayi na janyewar dakarun Burtaniya daga Iraqi,yana mai cewa ya kamata gwamnatin Iran ta sani fa cewa,sojojin Burtaniya suna Iraqi ne karkashin Majalisar Dinkin Duniya,tare kuma da goyon bayan gwamnatin Iraqin kanta.

Hakazalika kuma a cewarsa sojojin na Burtaniya,zasu kasance har iyaka lokacinda aiyukan majalisar Dinkin Duniya a kasar ya kammala a kasar Iraqin,hakazalika zasu kasance a kasar iyaka lokacinda gwamnatin Iraqi ta bukace su.

Blair yace,kira da ministan harkokin wajen Iran Manusher Mottaki yayi,na janyewar sojojin Burtaniya daga Iraqi,wata hanya ce ta janye hankalin kasashen duniya daga batun nukiliya na Iran.

Ita kuma Angela Merkel cewa tayi,Iran ta wuce gona da iri game da shirin nata na nukiliya da kasashen yammaci suke ganin kokari takeyi na kera makaman kare dangi.

Game da batun gidan fursunan gwale gwale na Guantanamo kuwa,Tony Blair yace,yana nan akan bakansa na cewa,batun Guantanamo,batu ne da dole a fuskance shi ko ba dade ko ba jima.

Blair yayi kwatankawacin wannan jawabi gaban majalisar Burtaniya a watan nuwamban bara,lokacinda wani dan majalisa yayi kira da a rufe Guantanamo.

Wani rahoton hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisa Dinkin Duniya dai,ya bukaci rufe Guantanamo dake dauke da fursunoni 500,wadanda rahoton yace ana azabtar da su.