1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Wakilan Majalisar Dokokin Jamus A Sudan

July 8, 2004

A ziyarar da suka kai kasar Sudan wakilan jam'iyyar hamayya ta CDU sun yi kira ga gwamnati a fadar mulki ta Khartoum da ta dauki nagartattun matakai domin shawo kan rikicin kasar a cikin gaggawa

https://p.dw.com/p/BviI

Takanas bayan saukarsu a filin jiragen saman Berlin wakilan jam’iyyar CDU Arnold Vaatz da Hartwig Fischer suka zarce zuwa taron manema labarai. An dai lura da kurar tafiyar dake tattare da su bayan balaguro na yini hudu a kasar ta Sudan. A lokacin da yake bayani Arnold Vaatz ya ce tuni aka fara ganin tasirin matsin kaimin da kungiyoyi na kasa da kasa ke yi akan gwamnatin Sudan, inda ya kara da cewar:

Na yi imanin cewar gwamnatin Sudan na da cikakkiyar niyyar shawo kan rikicin kuma ta sikankance da kurakuranta. Kazalika na yi imanin cewar zata yi bakin kokarinta wajen wajen wanzar da shawarwarin da ta samu daga Colin Powell da Kofi annan.

A dai halin da ake ciki yanzu an daina hana ruwa gudu ga ayyukan kungiyoyin taimakon jinkai kamar dai kungiyar likitoci ta kasa da kasa a cewar Hartwig Fischer. Ya ce bayan musayar yawun da suka yi da wakilan gwamnatin Sudan a fadar mulki ta Khartoum shi da takwaransa sun zarce zuwa Darfur domin ran gadin sansanoni dabam-dsabam da aka tanadar wa ‚yan gudun hijira. To sai dai kuma ko da yake sun samu kafar tattaunawa da mutane da dama da lamarin ya shafa amma fa sun lura da ‚yan leken asirin dake musu rakiya domin tsegunta wa gwamnati ire-iren abubuwan da suka tattauna. Dukkan wakilan na jam’iyyar Christian Democrats sun ziyarci sansanonin ‚yan gudun hijira a arewaci da kudancin Sudan da kuma lardin Darfur dake yammacin kasar. Fischer ya ce halin da ake ciki ya sun banbanta da juna a wadannan sansanoni. Domin kuwa a yayinda a can arewa al’amura suka fara sararawa kuma mutane ke da shirin komawa gida da zarar sun tabbatar da tsaron lafiyarsu, amma a can kudancin kasar ana fama da cunkoson ‚yan gudun hijira fiye da kima a wasu sansanonin da aka tanadar kuma kusan a kullu-yaumin sai an samu karin makaurata 500 zuwa 700 a wadannan yankuna. Wadannan mutane na tattare da fargaba da rashin sanin tabbas a game da makomarsu idan har sun koma gida. Amma duk da haka Hartwig Fischer ya kara da cewar:

Ina tattare da kwarin guiwar cewar gwamnati a fadar mulki ta Khartoum zata tashi tsaye wajen shawo kan rikicin kasar Sudan da ya ki ci ya ki cinyewa ganin yadda kungiyoyin kasa da kasa suka sa ido domin lura da salon kamun ludayinta. MDD a shirye take ta ba da goyan baya, sannan su kuma kungiyoyin taimako na kasa da kasa suna gudanar da ayyukansu, muddin al’amura suka ci gaba da tafiya akan haka to kuwa kasar Sudan zata samu wata kafa ta tsame kanta daga cikin wannan mawuyacin halin da take fama da shi tare da taimakon kawayenta abin da ya hada har da Jamus.