1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Zapatero a Ceuta da Melilla

February 1, 2006

Firamiyan kasar Spain, Jose Luis Rodriguez Zapatero ya kai ziyara a yankunan kasar na Ceuta da Melilla, wadanda ke cikin harabar kasar Marokko a arewacin Afirka. Ziyarar dai ita ce ta farko ta wani shugaban gwamnatin Spain din tun shekaru 25 da suka wuce. Ko wace irin alama Firamiyan ke son sanyawa da kai wannan ziyarar ?

https://p.dw.com/p/Bu1x
`Yan gudun hijira daga Afirka a sansanin Melilla.
`Yan gudun hijira daga Afirka a sansanin Melilla.Hoto: AP

Ta hakan ne dai mazauna garin Melilla suka tarbi Firamiyan kasar Spain, Jose Luis Rodriguez Zapatero, a lokacin da ya ziyarci yankin. Ban da dai `yan kasar Spain din, akwai kuma kusan baki dari 8 da ke zaune a sansanin `yan gudun hijira a garin. Su dai bakin, sun yi ta kururuwa ne na neman takardun izinin zama da na aiki, yayin da Firamiyan ke wucewa inda suke. In za a iya tunawa dai, a cikin watan Oktoban bara ne, daruruwan `yan gudun hijira daga kasashen Afirka suka yunkuri tsallake shingayen da aka dangace yankunan Ceuta da Mellillan da su, don hana su kutsawa cikinsu, su iya shiga Turai. An sami mutane da dama wadanda suka rasa rayukansu a wannan yunkurin, da kuma wadanda suka ji rauni. Su dai wadannan yankunan, duk da cewa mallakar Spain ne, amma a cikin harabar kasar Marokko suke. Halin da `yan gudun hijira ke ciki dai, sai muni ma ya kara yi, yayin da mahukuntan yankunan suka mai da su zuwa Marokko.

Saboda jamian kasar Marokkon, su ma a nasu bangaren sai suka kai su cikin hamada suka jibge su can ba tare da ba su ruwa ko abinci ba. Wannan lamarin dai ya janyo kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam ga gwamnatocin Spain din da na Marokkon. To ko wannan ne dalilin kai ziyarar Firamiya Zapatero a yankunan a halin yanzu ?

A garin Melilla dai Firamiyan ya bayyana cewa:-

„Zan dai karfafa matsayinmu na ci gaba da aiwatad da matakan tsaron da muka dauka da kuma tsaurara su. Kazalika kuma, za mu kyautata halin rayuwar duk jama’a a nan, don mu nuna cewa, mu `yan wata kasa ce, inda dokarmu da matakanmu na inganta jin dadin jama’a ke bambanta mu da sauran.“

Tun shekaru 25 da suka wuce dai, ba a taba samun wani shugaban Spain din da ya kai ziyara a yankunan ba sai wannan karon. Hakan kuwa ba abin mamaki ba ne, saboda har ila yau, kasar Marokko na da burin mamaye da kuma malllakar wadannan yankunan.

Jam’iyyun adawan kasar Spain din dai na zargin Firamiya Zapatero ne da nuna sassauci ga Marokko a kan wannan batun. Sabili da haka ne ma shugaban jam’iyyar adawa ta `yan mazan jiya ta kasar, Marianao Rajoy ya shawarci Firamiyan kafin ziyararsa a yankunan da cewa:-

„Kamata ya yi ya bayyana abin da kowa ya sani, wato na cewa Ceuta da Melilla yankuna ne na Spain, wadanda kuma dole ne a dau jama’arsu a matsayi daya da na sauran kasarmu. Dukkanmu dai na da hakkin daya na samun kariya da kulawa daga kasar. Ina fata dai, zai bayyana hakan a zahiri, kuma dalla-dalla ta yadda kowa zai fahimce shi.“

A kan yankunan Ceuta da Melillan ne dai, Spain da Marokko ke samun baraka a huldodin dangantaka tsakaninsu. Mazauna yankunan biyu na ta kara nuna damuwarsu ne a kan yadda makomarsu za ta kasance nan gaba. Mafi yawansu na fargabar cewa, wata rana za mika ikon harabobin ne ga Marokko.

Sai dai, da wannan ziyarar, Firamiya Zapatero na kokarin sanya wata alama ne ta nuna wa mazaunan cewa ba a manta da su ba. Kuma suna da cikakken `yancin da ko wane sauran dan kasar Spain ke da shi.