1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080409 Zuma Präsident Südafrika

April 15, 2009

Tsohon mataimakin shugaban Afirka ta Kudu na samun karɓuwa tsakanin al'umomin ƙasar, gabanin zaɓen ƙasa baki ɗaya

https://p.dw.com/p/HXDU
'Yan jam'iyyar ANCHoto: AP

Bisa dukkan alamu dai Jacob Zuma shine zai kasance shugabancin ƙasar Afirka ta kudu bayan zaɓen da zai gudana ranar 22 ga wannan wata na Afrilu. Sai dai ana cigaba da dasa ayar tambaya dangane da makomar ƙasar idan hakan ya tabbata.


Tun 'yan watanni da suka gabata nedai al'ummomin Afrika ta kudun, da masu kallo na ƙasashen ketare da ma ƙwararru ta fannin tattalin arziki ke dasa ayar tambaya dangane da ko hakan labari ne mai kyau wa wannan ƙasa?


Zuma dai ya kasance mutum ne daya bayyana wasu halayya na samun karɓuwa tsakanin jama'a fiye dana sauran shugabanni ko kuma 'yan takara da suka gabata.Kasancewarsa mai kwarjini ana bayyanashi da kasancewa "mai jama'a".

Jacob Zuma ANC
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan ƙabilarsa ta Zulu dai suna mara masa baya, duk da zargin da masu adawa keyi masa na rashawa da rikicin cinikin makamai daya kaishi gaban kuliya.Inda ya fito, Nkandla dai wani karamin gari ne a KwaZulu-Natal dake yankin kudancin ƙasar. Kuma dubban magoya bayan Zuma sanye da rigunan dake dauke da hotonsa sunyi dafifi cin annashuwa da murna.


Wannan yanki dai yana fuskanci tashe-tashen hankula lokacin da aka gudanar da zaɓen ƙasa na farko a shekarata 1994 ,sai gashi a yau ɗan asalin yankin ya fito domin takarar kujerar shugaban ƙasa.

A wannan gari dai ana iya cewar tamkar Zuma ya lashe kuri'unsu, kasancewar kusan jami'iyya guda ce ke mulki. A zaɓen ƙananan hukumomi da akayi a baya jami'iyyar al'umma ta Zulu-Inkatha, ita ce ta lashe kashi 91 daga cikin 100 na yawan kuri'u da aka kaɗa.

To sai dai shin wanene Jacob Zuma kuma yaya ya taso a wannan gari? Marimothu Subamoney ɗan jarida ne a gidan rediyon SABC....

Südafrika Jacob Zuma vor Gericht
Ɗan takara Jacob ZumaHoto: AP

" A gaskiya Zuma ya taso cikin hali mawuyaci.Kasancewar mahaifiyarsa aikatau ce a cikin gida, bai samu damar samun ili a shekarunsa na yaro ba.ya kasance shugaban yara a makaranta daga baya, kana yayi kokarin shiga harkokin siyasa, inda ya hadu da fushin sojoji wanda ya kaiga a cafke shi inda aka kai shi kurkun da ake tsare masu adawa da nuna banbancin launin fata, inda aka rufe Nelson Mandela na tsawon shekaru 27."


Afirka ta Kudu dai ta kasance ƙasa ce wadda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu, baya ga wasu miyagun ayyuka da ƙasar tayi kaurin suna akai. Kana ko yaya sabon shugaban zai tinkari matsalar tattalin arziki da sauran ƙasashen duniya ke fama da su. Wasu 'yan garin na Nkandla sun tofa albarkacin bakinsu.

" Na san shi yana da kirki, kuma mutum ne mai tausayawa talakawa. Irin mutumin da muke muradi kenan. Wataƙila zai gina mana makarantu, da nufin taimakawa mabukatu."


"Akwai zargi na rashawa da sauran laifuffuka a kansa, a ganina ba mutumin kirki ba ne a matsayin shugaban ƙasa."

Jami'iyyar ANC dai ta yi ƙaurin suna a Afirka ta Kudu duk da cewar har yanzu ɗan takara kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Jacob Zuma na samun suka.


Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Yahouza Sadissou Madobi