1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙalubalen da ke gaban taron AU

Usman ShehuJanuary 23, 2014

Tashe-tashen hankula a wasu ƙasashen Afirka, za su kankane taron shugabanni na bana, saɓanin bunƙasa noma kamar yadda aka tsara

https://p.dw.com/p/1AwKs
AU-Sondergipfel Abuja Gruppenbild
Hoto: DW/U. Musa

Bisa yadda aka tsara dai taron shugabannin ƙasashen Afirka na shekara-shekara da zai guda na a Addis Ababa babban birnin ƙasar Habasha, ya kamata ace an tattauna batun inganta noma, domin samar da wadataccen abinci a nahiyar. To amma sai dai har yanzu, batun tashe-tashen hankula a ƙasashen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Sudan ta Kudu, su ne gaba a jadawalin taron. ko da yake a yau Alhamis akwai alamar ɓangarori da ke gaba da juna, sun cimma matsaya, da ta kai suka sa hannu yarjejeniyar tsagaita wuta. To amma dai asalin rikicin abu ne ya daɗe a sabuwar ƙasar.

Tuni dai aka yi wa jiragen ƙasa da ke sintiri a birnin Addis Ababa fintin da ke ɗauke da alamar taron shugabannin ƙungiyar ta AU, mai laƙabin nahiyar Afirka mai bunƙasar noma. Amma lamarin ba haka yake ba, kamar yadda aka ji daga bakin Dakta Aisha Abdullahi, kwamishiniyar harkokin siyasa a ƙungiyar Tarayyar Afirka. Wanda a gabanin taron ta faɗawa tashar DW cewa, batun Sudan ta Kudu na gaba a taron nasu

Bildergalerie Südsudan Der jüngste Staat der Welt versinkt im Chaos
Hoto: DW/J.-P.Scholz/A.Kriesch

"Manufar mu ita ce, a samu dakatar da rikicin, don kawar da zubar da jini da ke faruwa. Domin a dawo da zaman lafiya a ƙasar"

To sai dai bisa ga dukkan alamu bisa sauri a ranar Alhamis ɗinnan, ɓangaren 'yan tawaye da gwamnati suka nuna alaman samun masalaha. To amma wannan bawai yana nufin zaman lafiya ta samu a ƙasar Sudan ta Kudu da rikici ya yi kanta, a cewar Jakkie Cilliers darakta a cibiyar nazarin harkokin tsaro da ke Pretoria.

"Rikicin Sudan ta Kudu ya yi ƙamari, don lamari ne da ke da wuyan warwarewa cikin sauri. Kuma abu ne da zai dauke mu shekaru masu yawa. Don haka taron AU zai duba dukkan hanyoyin da suka kamata, domin samun tallafi daga ƙasa da ƙasa da kuma a cikin ƙashen na Afirka. Amma dai bana jin cewa za mu iya warware rikicin a cikin garamin lokaci"

Sai dai a cewar kwamishiniyar harkokin siyasa a ƙungiyar ta AU Aisha Abdullahi, taron na su zai kasance da nasara.

"Za mu tabbatar da zaman lafiya da lumana, ya sake dawowa a wannan jaririyar ƙasar, cikin gaggawa"

To amma kakakin ma'aikatar harkokin wajen Habasha, ƙasar da a yanzu ke shugabantar ƙungiyar AU, yace duk da matsalolin da ke gaban shugabanni, akwai nasarorin da aka samu bara a cikin ƙasashen Afirka, wanda kuma bai kamata taron ya manta da su ba.

Zentralafrikanische Republik Interimspräsidentin Catherine Samba-Panza 23.01.2014
Hoto: Reuters

"A bara mun samu nasarori, kamar zaɓen da ya guda a kasar Kenya, Madagaskar da kuma ƙasar Mali, kuma waɗannan dole su kasance a cikin jadawali"

Duk da irin waɗannan nasarori, amma baya ga rikicin Sudan ta Kudu, babbar matsalar da ake fiskanta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wanda shi ma, a cewar jakadan ƙasar Faransa a Bangui, kawo yanzu ba a kai ga shawo kan ricin ba, duk cewa an zaɓi magajiyar birnin Bangui Catherine Samba-Panza, ta jagoranci gwamnatin wushin gadi. Amma fa har yanzu ana ci-gaba da kisan jama'a a ƙasar, kuma rarrabuwar kawuna tsakanin ɓangarori masu gaba yana da girma.

Mawallafa: Ludger Schadomsky/ Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani