1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙaramin jakadan Italiya a Libiya ya sha daga hari

January 13, 2013

Ƙaramin jakadan da ke a birnin Benghazi da ke a yankin gabashin ƙasar ya ƙetare rijiya da baiye baiye, sakamakon wani hari da aka kai a kan motarsa.

https://p.dw.com/p/17J5F
A security officer points to gun shots on the window of the Italian consul's car after it was shot by unknown assailants in Benghazi January 12, 2013. An Italian consul came under fire in his car in the eastern Libyan city of Benghazi on Saturday but was unhurt, the Italian Foreign Ministry said. REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA - Tags: POLITICS CRIME LAW) // eingestellt von se
Hoto: Reuters

Wasu mutane ne ɗauke da makamai da ba a tantance ko su wanene ba suka buɗe wuta a kan motar jakadan wacce harsashi ba ya iya hudawa. Jakadan Guido de Sanctis na yawo ne a cikin garin a lokacin da 'yan bindigar suka buɗe masa wuta, sai dai babu wani wanda ya samu rauni daga cikin waɗanda ke cikin motar. Wannan hari dai na zuwa ne watanni ƙalilan bayan harin da masu kishin addini suka kai a ofishin jakadancin Amurka wanda a kan sa, suka kashe jakadan da wasu mutane guda ukku.

Sanctis ɗan shekaru 51 da haifuwa na a birnin Benghazi tun lokacin da aka fara yin boren da ya kifar da gwamnatin Mouammar Kadhafi a shekara ta 2011 kuma a makon gobe aka shirya zai fara aiki a sabon mazaunin da aka kai shi a ƙasar Qatar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal