1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin dakarun zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Jane McintoshDecember 25, 2013

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri'a amincewa da ninka adadin dakarun kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu daga dubu bakwai zuwa dubu 12.

https://p.dw.com/p/1Agbk
Südsudan Juba Ausschreitungen Flüchtlinge UN 16.12.2013
Hoto: Reuters

Manbobin kwamitin sulhu guda 15 sun amince da ƙudirin da gaggarumin rinjaye tare da yin kira ga shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar,da su dakatar da buɗe wuta tare da soma tattaunawa ba tare da ɓata lokaci ba. Domin kawo ƙarshen rikicin ƙabilancin da ake yi tsakanin 'yan ƙabilar Nuer da Dinka wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusa dubu.

Kwamitin ya gaggauta ƙara yawan adadin dakarun ne kwana ɗaya bayan da aka gano wani katafaean kabarin da aka binne gawarwakin mutane sama da 70 a wasu garurruwan ƙasar. Babban sakataran Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon ya ce ɗaukar matakin zai taimaka a kare rayukan fararan hula.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe