1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen taron G 8 a Saint-Petesbourg

July 17, 2006
https://p.dw.com/p/BuqE

Yaƙi tsakanin Isra´ila da Hezbollah, na daga batutuwan da su ka mamaye taron ƙungiyar G8, da ya haɗa shugabanin ƙasashe 8 mafi ƙarfi tattalin arziki a dunia.

A tantanwar da su ka yi yau, shugabanin, sun bayyana wajicbin tura rundunar shiga tsakani a kudancin Labanon.

Saidai, duk da yarjejeniyar da su ka rataba hannu a kai jiya, a game da da wannan yaƙi, ƙasashen G8, na fuskantar rarrabuwar kanu.

Shugaban ƙasar France Jaques Chirac, ƙarrara ya nuna adawa da matsayin Amurika, na ɗora lefin ɓarkewar yaƙin a kan ƙungiyar Hezbollah kaɗai.

Saidai baki ɗaya sun bukaci ɓangarorin su ajje makamai, sanan Hezbollah ta yi belin sojojin Isra´ila da ta ke garkuwa da su.

A wani baben kuma, taron Saint Petesbourg, ya tanttana a kan matsalolin tattalin arzikin ƙasashen Afrika.

A dangane da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, ƙasashen G8, sun yi kira ga hukumomin Teheran, su amince da tayin da, ƙasashe EU, Amurika, Rasha da China su ka yi masu a watan da ya gabata.

A danagane da badakkalar makamami maus lizzami da Korea ta Arewa ta harba akmakonda ya gabata, Rasha da China sun bayana yiwuwar warware rikicin ta hanyoyin diplomatia.