1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen Afirka na buƙatar aiki tare wajen magance ɗumamar yanayi

November 22, 2013

Masana yanayi sun shawarci ƙasashen Afirka da su yi aiki tare wajen ganin sun tunkari matsalar ɗumamar yanayi duba da irin matsalar da ta ke tattare da ita.

https://p.dw.com/p/1AMj5
Hoto: Reuters

Wannan kiran dai na zuwa ne daidai lokacin da wakilai na ƙasashen duniya suka kammala taro kan ɗumamar yanayi a birnin Warsaw na ƙasar Poland wanda Majalisar Ɗinkin Duniya kan shirya don duba batun na ɗumamar yanayi. A bana dai da dama daga cikin masu hallartar wannan taron na ganin cewar ƙasashen Afrika sun amfana matuƙa dangane da irin abubuwan da aka tatauna a zauren taron musamman ma dai idan aka yi la'akari da alƙawuran da aka lashi takobin cika wa ƙasashen Afirka dangane da wannan yaƙi da ake da dumamar yanayi.

Nura Jibo muƙaddashin shugaba ne na wata cibiya da ke gudanar da bincike kan ɗumamar yanayi a Najerya, ya kuma shaida wa DW cewar daga cikin irin abubuwan da Afirka za ta ci moriya har da wani tallafi na kuɗi da horo kan dabbarun yaƙi da ɗumamar yanayi.To sai dai duk da cewar Afirka za ta amfana da wannan tallafi, a hannu guda Melita Steele, jami'a a wata ƙungiya ta yaƙi da ɗumamar yanayi ta Greenpeace ta ce dole ƙasashen nahiyar Afrika musamman ma dai gwamnatoci su ma su tsaya kan diga-digansu wajen ganin sun ba da babbar gudumawa wajen ganin an yaƙi wannan matsala da ke ci gaba da ƙassara nahiyar.

Peter Altmaier Bundesumweltminister Klimakonferenz in Warschau 20.11.2013
Wakilin Jams da sauran takwarorinsa wajen taronHoto: DW/A. Rönsberg

Ta ce ''akwai buƙatar Afirka ta Kudu alal misali ta rage irin hayaƙin da ta ke fiddawa wanda ke da illa ga sararin samaniya saboda yanzu haka ƙasar na ta faɗaɗa aikin tonon kwal a ƙasar ta hanyar gina sabbin wuraren sarrafa shi, kazali ya kyautu ƙasashen Afirka su kasance bakinsu ya zo ɗaya idan ana tattaunawa kan batun magance dumamar yanayi a nahiyar''b Yayin taron na bana dai, an ɗan samu saɓani na ra'ayi dangane da wannan yaƙi da ake na ɗumamar yanayi lamarin da ya sanya wasu ke ganin cewar ba a kai ga cimma abubuwan da aka ƙuduri aniyar yi ba, yayin da mutane irin du Nura Jibo da ke zaman muƙaddashin shugaba na wata cibiya da ke gudanar da bincike kan ɗumamar yanayi a Najeriya ke cewar ba za a ce an gaza cimma komai a taron ba sai dai nasarar da aka cimma za ta iya kasancewa a cike da matsala.Ya ce ''China da Amirka sun yadda su rage irin yawan kwal din da su konawa wanda ke da illa ga sararin samaniya sai dia sun ce dole wasu ƙasashe irin su Indiya da Jamus da makamantansu su ma su kawo ƙarshen hayaƙin da suke fiddawa wanda ke da illa, lamrin da ya sa ake ganin kai wa ga cimma hakan abu ne mai wuya.

Umweltverbände verlassen Klimakonferenz in Warschau
'Yan kungiyoyin fararen hula da suka kauracewa taronHoto: AFP/Getty Images

Yayin da wasu ke ganin za a iya cewa an cimma nasara duk kuwa da sarƙakiyar da ke tattare da ita, ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da ke yaki da ɗumamar yanayi na kallon taron a matsayin na shan shayi don kuwa a cewarsu an gaza tankwara ƙasashen da ke kan gaba wajen fidda hayaƙin da ke illata muhalli, wannan ne ma ya sanyasu ficewa daga zauren taro a wai mataki na nuna takaicinsu.Yanzu haka dai da dama na zuba idanu don ganin yadda za a kai ga warware wannan matsala da ke zaman barazana ga ƙasashen duniya baki ɗaya.

Daga ƙasa za iya sauraron wannan rahoto haɗe da hirarar da Pinado Abdu ta yi da Dr Ado Mukthar Bichi wani mallami a sashen illimin kimiyar muhalli a jami'ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin jihar Kano dake Wudil.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane