1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙin amincewa da Hagel a matsayin sabon sakataren tsaron Amurka

February 15, 2013

'Yan Republican sun yi ruwa da tsaki wajen ganin cewa sun jinkirta fara aikin Chuck Hagel a matsayin sabon sakataren tsaro Amurka, a inda suka ki amincewa da shi.

https://p.dw.com/p/17eg0
Hoto: Reuters

Jam'iyar Republican ta ƙasar Amurka ta haddasa tsaiko a yunƙurin da majalisar dattawa ta yi na amincewa da mutumin da shugaba wannan ƙasa ya zaɓa a matsayin sakateren tsaronsa wato Chuck Hagel. Kuri'u 58 gwanin na Obama ya samu lokacin da 'yan majalisan dattijai suka kaɗa ƙuri'a, alhali ya na buƙatar ƙarin kuri'u biyu kafin ya haye. Ana kyautata zaton cewar majalisar ta dattijjai za ta iya amincewa da sabon sakateren na tsaron Amurka a zaman da za ta yi a ranar 26 ga wannan wata na Fabreru.

Shi dai Hagel wanda zai maye gurbin Leon Panetta tsohon dan majalisan dattijai ne. Sai dai jam'iyarsa ta na adawa da nada shi da aka yi a wannan mukami. 'yan Republican na zarginsa da adawa da yaƙin Iraƙi da kuma ƙin kaɗa ƙuri'ar amincewa da takunkuman karya tattalin arziki da Amurka ta kakabawa Iran.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar