Ƙungiyar NATO na gudanar da taro a birnin Brussels
April 1, 2014Talla
A wannan Talatar ce (01.04.2014) Ministocini zasu duba yiyuwar ƙara karfin ƙungiyar tsaron ta NATO a yankin Turai ta Gabas. Inda kuma a wannan rana ce NATO za ta fara wani sabon attisaye, na sa ido kan sararin samaniya a yankin Vilnuis, attisayan da zai samu halartar jiragen yaƙi na turai da Amirka. A hannu ɗaya kuma shugabannin diplomasiyar ƙasashen Jamus, Faransa, zasu yi wani zaman taro a dabra da taron ministocin harkokin wajan membobi a ƙungiyar NATO.
Daga na shi ɓangaren yau ne ake sa ran kamfanin nan, mai Fitar da iskar Gaz na ƙasar Rasha, zai tsawala kuɗin Gaz ga ƙasar ta Yukren.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane