1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓarakar jami'yyar PDP mai mulki a Najeriya

December 9, 2013

Masu nazarin siyasa na hasashen cewar rikicin PDP ya kai wani matsayi bayan da gwamnoni 13 suka buƙaci shugaban jami'yyar Bamanga Tukur ya sauka.

https://p.dw.com/p/1AVlh
Nigeria Plakat Präsident Goodluck Jonathan Archiv 2011
Shugaba Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

A yanayin da ke nuna alamun ƙara dagulewar rikicin jam'iyyar PDP da ke mulkin Najeriya, gwamnonin 13 na jam'iyyar sun bayyana buƙatar lallai sai shugabanta jam'iyyar Bamanga Tukur ya sauka daga muƙamminsa, muddin ana son samun masalaha. To ƙurar rikicin na jam'iyyar PDP dai tana ƙara tirniƙewa ne duk da ziyarar da fadar shugaban Najeriyar ke yi na ganin ta samu shawo kan gwamnonin nan bakwai da ke ƙara jan daga a kan ɓalewar da suka yi daga jam'iyyar, lamarin da ke ci gaba da yi mummunan tasiri ba kawai ga PDP ba har ma ga siyasar Najeriyar.Domin kuwa akwai baiyanai da ke nuna cewar a yanzu yawan gwamnonin ya kai har su 13 dukkaninsu a cikin jam'iyyar ta PDP da ke buƙatar lallai sai a yi awon gaba da shugaban na PDP Alhaji Bamangta Tukur daga muƙaminsa ya zamo abin da a yanzu yafi tsone wa ya'yyan jam'iyyar da dama ido, domin ganin salon da rikicin ke ɗauka.

Alhaji Nasiri Isa Abubakar jigo ne a ɓangaren Kawu Baraje na PDP wanda shi ne ma tsohon sakatren tsare-tsare na ɓangaren na Kawu Baraje, inda biyar daga cikinsu suka koma jam'iyyar adawa ta APC saboda adawar da suka daɗe suna yi abin da suka kira saba ƙaidaojojin jam'iyyar ta PDP, ya ce ai dama can buƙatar sai Bamanga ya sauka daga shugabancin PDP na cikin buƙatunsu kuma suna da dalilan da yasa suka dage a kan haka.

‘'Ai dama maganar Bamanga ya bar shugabancin PDP shi ne ma gaskiyyar buƙatar da muka gabatar wa shugaban ƙasa, kuma dalil;I shi ne duk waɗannan matsaloli da aka samu sun afku ne a ƙarƙashin jagorancinsa, kuma abubuwan nan suka rinƙa faruwa haka, an kori gwamnan Sokoto, an kori gwamnan Rivers an samu rigingimu a Adamawa. Don haka gaskiyya ta bayyana kenan za'a ce don waɗanda ba su yarda da abubuwa da muka faɗa a kan Bamaga cewa ba muna ƙin sa ba ne a yau suma sun bi layi , muna ƙin sa ne don abubuwa da yake yi da ke kawo raraubuwan kawuna a cikin jam'iyya''.

Masu nazarin sun ce mai yiwuwa rikicin ya kai ƙololuwa wannan karon

Ko da yake wasu na hangen ƙara zafin da rikicin jam'iyyar ke yin a iya zama alamar kai wa ga ƙololuwarsa, to amma ga shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukuru da tuni da daɗe wa yake ƙara jajircewa a kan wannan lamari, na zama wanda ke nuna bafa gudu kuma ba ja da baya. Domin kuwa a wani jawabi day a yi a makon jiya ƙarara a fili ya bayyana hakan har ga masu goyon bayan ya ci gaba da jagorancinsa.'Kar ka ji tsoro, ka da ku ji tsoro haka aka ce a zauna a yi shiri,da shi.''

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Hoto: DW/U.Haussa

Ƙara jan daga da gwamnonin ke yi a kan batun yadda ake tafiyar da jam'iyyar na zama manuniya na shiga makoma ta rashin tabbas ga jam'iyyar ta PDP da ta kwashe shekaru goma sha huɗu tana mulki a Najeriyar, amma kuma rigingimun cikin gidan da suka tasota a gaba ke jefa tsoron darewarta gida biyu. A yayin da duk wannan ke faruwa ga Tafida Mafindi wakili a kwamitin zartaswar na jam'iyyar ta PDP na mai bayyana illar da wannan rikici ke da shi, musamman a dai dai lokacin da Najeriyar ke fuskantar babban zaɓe a 2015.‘'Irin wannan fita da barazana da ake yi suna ƙaara ɓata sunan jam'iyyar PDP ga al'ummar Najeriya, kuma duk abin da ake yi barazana ne don haka zama a gyara a sake daidaita wa yafi a kan tafi ya a lallace har lokacin da zaɓen zai zo''

Bayyana ta ke a fili cewa gwamnonin jam'iyyar ta PDP da suka doshi shugaban Najeriya da wannan buƙata suna ƙara shirin ta ware ko waraye musamman ma dai waɗanda suka bursuna wa fuskokinsu hoda ta hanyar tsunduma jam'iyyar adawa ta APC da ake ganin na zama babbar barazana da PDP ba ta taɓa fuskanta ba a fagen siaysar Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani