1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

2006: Shekarar Mozart

January 3, 2006

A wannan shekarar ne za a yi bikin zagayowar shekaru 250 na haihuwar shahararren mawallafin wakokin nan Wolfgang Amadeus Mozart. An haifi Mozart ne a ran 27 ga watan Janairun 1756 a garin Salzburg da a halin yanzu ke kasar Austriya. Ko yaya halin rayuwar wannan mawakin ya kasance, kafin mutuwarsa a ran 5 ga watan Disamban 1791 ?

https://p.dw.com/p/BvU3
Wolfgang Amadeus Mozart
Wolfgang Amadeus MozartHoto: dpa - Bildfunk

A ran 27 ga watan Janairu na shekara ta 1756 ne aka haifi Wolfgang Amadeus Mozart a garin Salzburg. Tun yana dan yaro ne dai ya nuna basira wajen wallafa wakoki. Ya kuma sami nasara matuka a lokacin rayuwarsa. Amma ya mutu ne a talauce, a birnin Vienna, a ran 5 ga watan Disamban 1791. To sai bayan mutuwarsa ne aka fahhimci basirar da ke kunshe cikin tsarin wallafa wakokinsa, wato irin wakokin nan da aka fi sani da suna classical music a turance. A halin yanzu dai, wakokin Mozart sun yi tashe a yankuna da dama na duniya, musamman ma dai inda aka fi jin irin wakokin classical music, kamar a kasashen Yamma, da Asiya, da Rasha da kuma arwewacin Amirka.

Tun Mozart na da shekaru 5 ne mahaifinsa, Leopold, wanda shi ma malamin fannin wakoki ne, ya gane basirar da dansa ke da ita. Sabili da haka ne ya yi ta yawo da shi da kanwarsa zuwa kasashen ketare don su yi wasanni. Har dai zuwa shekarar 1766, uban ya ziyarci manyan biranen Turai da su, kamar Paris da London da kuma Den Haag. Amma kafin haka ma, sai da Mozart ya fara yin wasanni a cikin gida, inda ya kayatad da jama’a a biranen Munich, da Vienna da Augsburg da kuma Frankfurt.

Tarihi dai na nuna cewa, shi uban Mozart din, wato Leopold, mutumin birnin Augsburg ne na nan Jamus. Sabili da haka ne kuwa, a shirye-shiryen da aka tsara na bukukuwan cika shekaru dari 2 da 50 da haihuwar shahararren mawakin, za a fara shagulgulan ne ne a wannan birnin, inda kuma shugaban kasa Horst Köhler ne zai kasance babban bako.

A birnin Wienna da kuma garin haihuwarsa Salzburg ma, za a yi bukukuwa daban-daban.

Kafin dai mutuwarsa, Mozart ya wallafa ayyukan wakoki fiye da dari 6. Har ila yau dai ra’ayin masana tarihi ya bambanta a kan dalilin mutuwarsa. Wasu sun ce guba aka ba shi, wasu kuma sun ce ya kamu ne da cutar tùnjéerée.

A ran 27 ga wannan watan ne za a yi wani gagarumin biki a birnin Vienna, inda shahararrun mawaka na yanzu za su halara. Kazalika kuma gidajen talabijin da dama na duniya za su nuna bikin kai tsaye a cikin shirye-shiryensu.