1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ƙasar Mali 'yan tawayen sun fara rusa gadoji

Usman ShehuJanuary 25, 2013

'Yan tawayen Mali sun rusa wata gada mai hamimmanci a yaƙin ƙasar, inda suka yanke han'yar Bamako izuwa birnin Gao, tungar 'yan tawayen

https://p.dw.com/p/17RTC
Fighters from the Al Qaeda-linked Islamist group MUJWA, who are travelling with a convoy including Burkina Faso foreign minister Djibril Bassole, stand guard in Gao, northern Mali, August 7, 2012. Bassole, the lead mediator in regional efforts to end unrest in Mali, told rebels there that they had to cut ties to "terrorist movements" like al Qaeda before any peace talks could begin, when he travelled to the rebel-held north for the first time on Tuesday. Picture taken August 7, 2012. REUTERS/Stringer (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
'Yan tawayen MUJWA a birnin Gao kasar MaliHoto: Reuters

Yan tawayen ƙasar Mali sun rusa wata gada wanda ke da mahimmaci a yaƙin ƙasar. Gadar wanda yan tawayen suka rusa, itace ta haɗe tungar yan tawayen a birnin Gawo da birnin Bamako, kuma itace dakarun ƙasashen waje za su iya bi cikin sauƙi, don kai ga birnin Gawo dake hannun yan tawayen. Rohotanni suka ce a daren jiya yan tawaen suka rusa gadar Tassiga wanda ke kilo mita 95 daga kan iyakar Jamhuriya Nijar da Mali, kana tana kilo mita 150 kacal daga Bamako babban birnin ƙasar Mali. Dama can an tura dakarun jamhuriyar Nijar 500 da na ƙasar Chadi 2000, domin su bude wani fagen daga ta gabacin Mali. Wani direba Abdou Maiga wanda yaga gadar da aka rusa, yace yanzu babu wanda zai fito daga Nijar ya tafi Gao ta wannan hanyar. An dai rawaito jami'an tsaro a jamuhrioyar Nijar na cewa, har yanzu akwai wata doguwar hanya da za iya zagyowa don isa birnin Gao sai da kam tana da ɗan karen nisa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu