1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A haramtawa Moroko shiga gasar kofin Afirka

November 11, 2014

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Afirka ta haramtawa kasar Moroko shiga gasar neman cin kofin kwallon kafa na Afirka da ke tafe

https://p.dw.com/p/1DlWJ
Issa Hayatou in Marokko
Issa Hayatou shugaban hukumar kwallon kafa ta AfirkaHoto: F. Senna/AFP/Getty Images

Wata sanarwa da hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta fitar bayan kammala taro a birnin Alkhira na kasar Masar, ta bayyana cewa tunda dai Moroko ta fasa karban bakwancin gasar cin kofin kwallon kafan Afirka to kuwa ba za ta shiga gasar ba. Moroko dai ta sanar da cewa, ta fasa karban bakwancin gasar, a wani abin da gwamnatin kasar ta ce, wai tsaron bazuwar cutar Ebola ne yasa. Yanzu haka kungiyar CAF na ci gaba da tantance wata kasa da za ta karbi bakwancin gasar a bana.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo