1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Najeriya an yanke hukuncin ɗurin rai da rai kan wani ɗan ƙungiyar MEND

Usman ShehuJanuary 25, 2013

Kotun Tarayya dake Abuja ta samu Edmund Ebiware da laifi a harin Abuja na shekara ta 2010, inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai

https://p.dw.com/p/17Rnw
Image made available on 19 September of militants from the Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) as they patrol the volatile oil rich creeks of the Niger delta in Nigeria 18 September 2008. The Movement for the Emancipation of the Niger Delta claimed in a statement on 19 September 2008 it has attacked a pipeline operated by Shell. MEND declared 'war' on Nigeria's oil industry a week ago. EPA/GEORGE ESIRI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Mayaƙan ƙungiyar MENDHoto: picture alliance / dpa

A Najeriya wani kotun Tarayyar a Abuja ya yanke hukuncin aurin rai da rai kan ɗaya daga mutanen da aka zarga da kai harin ranar ɗaya ga watan Oktoban shekara ta 2010. Mutumin mai suna Edmund Ebiware jami'an leƙen asirin ƙasar ne suka kama shi a oteldin Belingua, kwana biyu bayan kai harin, wanda aka yi a dai-dai lokacin da ake gudanar da bikin samun yancin kan Najeriya.

Maishari'a Gabriel Kolawole a shari'ar da ta dauki sa'o'i ukku, ya zargi Ebiware da laifin ƙin faɗawa hukumomin da suka dace a ƙasar, duk da cewa yana sane da za a kaiwa ƙasar harin ta'addanci. Don haka aƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.

Wannan hukuncin dai bai yi wa wanda aka yankewa hukuncin daɗi ba, inda ya yi ta kururuwa, abinda ya sa jam'an tsaro suka yi amfani da ƙarfin don tura shi cikin mota, kana aka yi da shi izuwa kurkuku. Hukuncin ya zo ne, 'yan kwanaki bayan yankewa Herry Okah shugaban ƙungiyar yan bindiga ta yankin Niger Delta wato MEND makamancin wannan hukuncin a ƙasar Afirka ta kudu.