1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Najeriya ta tabbata an yanka ta tashi tsakanin gwamnati da Boko Haram

Abdourahamane HassaneNovember 6, 2014

Gwamnatin Najeriya ta yi amai ta lashe bayan da farko ta fito ta yi shelar cewar ta cimma yarjejeniya da Ƙungiyar Boko Haram,a yanzu ta ce zance ba haka yake ba.

https://p.dw.com/p/1DiN0
Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Tun da farko Mahukuntan Tarayyar Najeriya sun ce sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Ƙungiyar Boko Haram makwanni kusan biyu da suka gabata. Amma kuma daga bisani suka fito suka ce har yanzu da sauran tafiya. Hakan kuwa na zuwa ne bayan da Ƙungiyar Boko Haram ta ƙwace garin Mubi da ke cikin jihar Adamawa da ke a yankin arewa maso gabshin Najeriya,lamarin da ya saka al'ummar yankin cikin wani mawuyacin hali.